Waiwaye: Tsoffin hotunan tsohon Shugaban kasa Obasanjo da ke nuna shi jakadan Najeriya ne na kwarai
Tarihin Najeriya ba zai taba cikaba ba tare da sunan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba. Ebora na Owu kamar yadda ake kiransa ya yi aiki a matsayin shugaban Najeriya a mulkin soja tsakanin 1976 da 1979, kuma a matsayin shugaban farar hula tsakanin 1999 da 2007.
Legit.ng ta gabatar da tsofaffin hotuna guda biyar na tsohon shugaban kasar da ke nuna shi jakadan Najeriya ne na kwarai.
KU KARANTA KUMA: Manyan yara sun yi ruwan kudi a wajen wani liyafar biki da aka yi a Benin
1. Ya halarci taron koli a Gabon
A matsayinsa na shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya halarci taron shugabannin kasashen Afirka a Libreville da ke Gabon a ranar 13 ga watan Yulin 1977.
Ana iya ganin Laftanar-janar din lokacin yana fara’a yayin da yake sanye da kayan gargajiya.
2. Olusegun Obasanjo ya halarci wata ganawa da Jimmy Carter
Ana iya ganin shugaban na wancan lokacin tare da Jimmy Carter, shugaban Amurka na 39, wanda ya yi shugabanci tsakanin 1977 da 1981.
Kamar koyaushe, ana iya ganinsa yana bunkasa al'adun Afirka tare da shuɗiyar tufafinsa ta Yarabawa wacce ya saka zuwa wajen bikin yayin da takwaransa na Amurka ya saka kwat.
Wasu jami'an gwamnati da suka sanya kayan gargajiya suma sun halarci bikin.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rundunar sojoji ta kashe ‘yan ta’adda 73, ta ceto mutum 55 a Borno
3. Olusegun Obasanjo tare da Madeleine Albright
Shugaban da aka zaba ta hanyar dimokiradiyya a wancan lokacin ya kasance a New York, Amurka, don halartan Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya na 54 a ranar 24 ga Satumba, 1999.
An ganshi yana gaisawa da sakatariyar harkokin wajen Amurka Madeleine Albright.
4. Olusegun Obasanjo ya gana da Kurt Waldheim
Ana iya ganin tsohon shugaban kasar yana ganawa da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na hudu, Kurt Waldheim, wanda daga baya ya zama shugaban Austria.
An ɗauki hoto a cikin shekarar 1977.
5. Olusegun Obasanjo da Jimmy Carter
Laftanar na lokacin ya yi musabaha da shugaban Amurka na 39, Jimmy Carter, bayan tsohon shugaban ya yi jawabin maraba da shi yayin bukukuwa a Barikin Dodan.
Hoton Shugaba Buhari yana rawa da wata mace
A gefe guda, wani tsohon hoto na Shugaba Buhari yana more rayuwa lokacin da yake matashi ya haifar da zazzafan martani a shafukan sada zumunta.
Wani ma’abocin amfani da Facebook mai suna Ayo Ojeniyi ya dimauta yanar gizo da wani hoto wanda ba kasafai ake gani ba na Shugaba Buhari yayin da wani saurayi yake rawa da wata farar mace ba takalmi.
Da yake wallafa hoton, ya rubuta cewa:
"PMB ya kasance dan sharholiya sosai yayin da yake tasowa. A zamanin nan, ya kame kansa !!! Dube shi yana shanawa a wani liyafa lokacin da yake saurayi !!!!"
Asali: Legit.ng