El Rufai Ya Shiga Gidan Yari, Ya Gana da Tsohon Jami'in Gwamnatinsa da Aka Kama

El Rufai Ya Shiga Gidan Yari, Ya Gana da Tsohon Jami'in Gwamnatinsa da Aka Kama

  • Nasir El-Rufai ya ziyarci gidan gyaran hali na Kaduna don ganawa da tsohon shugaban ma’aikatansa, Bashir Saidu, wanda aka tsare
  • Legit Hausa ta rahoto cewa Bashir Saidu yana fuskantar tuhuma kan almundahana, wanda ya kai ga tsare shi a gidan gyaran hali
  • Tsohon gwamnan na Kaduna ya ki cewa komai game da tuhumar da ake yi wa Bashir yayin da ya tafi cikin motarsa bayan ziyarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ziyarci gidan gyaran hali na jihar domin ganawa da Bashir Saidu, wanda aka tsare a wurin.

Bashir Sa'idu dai shi ne tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Kaduna a lokacin da Nasir El-Rufai ya ke gwamnan jihar.

An hango El-Rufai a gidan yari yayin da ya kai wa tsohon shugaban ma'aikatansa da aka tsare
El-Rufai ya yi gum da bakinsa yayin da ya kai wa Bashir Sa'idu ziyara a gidan yarin Kaduna. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

Nasir El-Rufai ya ziyarci Bashir Saidu a gidan yari

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa cewa tsohon gwamnan ya isa gidan gyaran hali tare da wasu tsofaffin kwamishinansa uku da misalin karfe 10:19 na safe kuma ya tafi karfe 10:47.

Kara karanta wannan

Tsohon jami'in gwamnatin El Rufai ya shiga hannun jami'an tsaro a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyarar ta El-Rufai na zuwa ne bayan kama Bashir a ranar Litinin da gurfanar da shi a gaban kotun majistare da ke Rigasa, wanda ta ba da umarnin tsare shi kan zargin almundahana.

Tsofaffin kwamishinonin da suka yi wa tsohon gwamnan rakiya a wannan ziyarar sun hada da tsohon kwamishinan ilimi, Jafaru Sani.

Sauran sun hada da tsohuwar kwamishinar harkokin jin kai, Hafsat Baba da tsohon kwamishinan muhalli, Ibrahim Hussaini.

Tsohon gwamna El-Rufai ya yi gum da bakinsa

Da yake sanye da hula kore da doguwar riga mai haske, El-Rufai ya ki cewa komai game da ziyarar, kamar yadda wakilin jaridar ya bayyana.

Duk kokarin da aka yi don jin ta bakin tsohon gwamnan ya ci tura yayin da ya shiga daya daga cikin wata mota kirar Prado da ta yi masa rakiya.

Ziyarar El-Rufai ta jawo ce-ce-ku-ce

Ana zargin Bashir Saidu da almundahana da wasu laifuffuka da ba a bayyana ba, wanda hakan ya sa aka tsare shi a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan Mahadi Shehu kan zargi game da sojojin Faransa, ta fadi dalilai

Wannan ziyara ta tsohon gwamnan ta janyo ce-ce-ku-ce yayin da jama’a ke nazari kan dalilin tsare tsohon shugaban ma’aikatan.

"Ban taba satar ko kobo ba" - El-Rufai

A wani labarin, mun ruwaito cewa Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya shiga siyasa domin yi wa jama’a hidima, ba don neman kudi ko wawure dukiyar al’umma ba.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce ya gamsu da ayyukan da ya gudanar tun kafin ya zama gwamna, duk da zarge-zargen da ake yi masa.

El-Rufai ya ce zai iya rantsewa da Alƙur’ani idan sauran shugabanni sun yi hakan cewa ba su saci dukiyar talakawa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.