'Akwai Kalubale da Rigingimu': Malamin Musulunci Ya Yi Hasashen Shekarar 2025

'Akwai Kalubale da Rigingimu': Malamin Musulunci Ya Yi Hasashen Shekarar 2025

  • Malamin Musulunci ya yi hasashen shekarar 2025, yana mai gargadi kan matsalolin siyasa da tattalin arziki da ke bukatar kulawa na gaggawa
  • Farfesa Sabit Ariyo Olagoke ya nuna bukatar tsaurara tsaro da inganta ilimi, tare da hasashen rikice-rikice tsakanin manyan ‘yan siyasa
  • Malamin ya yi nuni da yiwuwar sauye-sauye masu kyau a harkokin tattalin arziki da noma a Oktoba da Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Shugaban darikar Shafaudeen-in-Islam, Farfesa Sabit Ariyo Olagoke, ya fitar da hasashen shekara ta 2025.

Malamin ya fadi manyan-manyan kalubale da gwamnati da al'umma za su fuskanta a sabuwar shekarar nan ta bana.

Malamin Musulunci ya yi hasashen abubuwan da za su faru a 2025
Sheikh Farfesa Sabit Ariyo Olagoke ya yi hasashen abin da zai faru a sabuwar shekarar 2025. Hoto: Professor Sabit Ariyo Olagoke, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Sheikh Olagoke ya yi hasashen shekarar 2025

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwa da aka gabatar wa manema labarai a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

PDP, Obi sun ba Tinubu lakanin samo waraka daga matsalolin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Olagoke ya nuna bukatar daukar matakan gaggawa don magance matsaloli da ka iya haddasa rikici.

Ya yi hasashen cewa watan Janairun 2025 zai kasance mai cike da ayyukan siyasa, inda alkawuran ‘yan siyasa za su yi tasiri sosai, tare da bukatar tsaurara tsaro.

A watan Fabrairu, ana hasashen ci gaba a fannin kasuwanci, yayin da za a fuskanci karin bincike kan ‘yan ta’adda da wasu kungiyoyin asiri.

Sai ya nuna a watan Maris za a samu ci gaban tattalin arziki da tallafi ga ilimi, za a kara kokarin kamo manyan masu laifi, yayin da gwamnati za ta yi aiki kan bin ka’idojin addini.

Ya ce kare hakkin dan Adam zai karu a watan Yuli, tare da kokarin daidaita ayyukan addini da tsare-tsaren tarbiyya.

Malamin ya yi hasashen watan Agusta mai albarka

A watan Agusta, ana hasashen noma za ta yi kyau, yayin da za a ci gaba da inganta ilimi da tsaro, musamman kan kafafen addini masu zamba.

Kara karanta wannan

'Ni jan biro ne maganin dakikin yaro,' Gwamna Fubara ya jijjige Wike da mutanensa

Sai dai ya ce Satumba za a samu rigingimu tsakanin ‘yan siyasa, amma ana hasashen ci gaba a bangaren tsaro da ilimi.

Sai kuma Oktoba za ta kasance wata mai cike da albarka a fannin noma da walwala.

A karshe, Disamba na iya zama wata mai cike da damar habaka tattalin arziki, tare da kira ga gwamnati ta tabbatar da tsaurara matakan tsaro.

Shehi ya magantu kan rigimar Nijar, Najeriya

Mun kawo muku cewa ana tsaka da rigima tsakanin Najeriya da Nijar, Sheikh Abubakar Malami ya yi martani.

Malamin ya koka game da yadda yan Nijar suke tsinewa Bola Tinubu da Najeriya saboda matsalar da ke tsakaninsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.