Tinubu Ya Dawo da Tsarin Makarantun Najeriya da Aka Soke Lokacin Yana Gwamna

Tinubu Ya Dawo da Tsarin Makarantun Najeriya da Aka Soke Lokacin Yana Gwamna

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da dawo da darasin tarihi a matsayin wajibi ga ɗaliban makarantun firamare da sakandare
  • Rahotanni sun nuna cewa an cire tarihi daga tsarin karatun Najeriya tun shekarar 2007, lamarin da ya ja suka daga masu ruwa da tsaki
  • Masana na ganin cewa sabon tsarin zai taimaka wa ɗalibai su fahimci Tarihi domin haɓaka haɗin kai da gina al'umma mai kishin kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin dawo da darasin Tarihi a matsayin darasi mai muhimmanci ga ɗaliban firamare da sakandare a Najeriya daga shekarar 2025.

An cire Tarihi daga tsarin karatun Najeriya tun a lokacin Olusegun Obasanjo a shekarar 2007, matakin da ya jawo martani da ƙorafe-ƙorafe daga al’umma.

Kara karanta wannan

PDP, Obi sun ba Tinubu lakanin samo waraka daga matsalolin Najeriya

Tinubu
Gwamnati ta dawo da darasin tarihi a makarantun Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a wani shirin tashar Channels Television na karshen shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a dawo da darasin Tarihi a makarantu

Ministan ilimi ya bayyana cewa cire Tarihi daga tsarin karatu a makarantu ya jawo babban gibi a fahimtar tarihin Najeriya musamman ga matasa.

Ministan ya ce:

“Shugaba Bola Tinubu ya yi umarni da a dawo da darasin Tarihi domin a saka shi cikin tsarin karatun ɗalibai na firamare da sakandare daga shekarar 2025.”

A cewarsa, matakin zai taimaka wa ɗalibai su fahimci tarihin ƙasa tare da ƙarfafa haɗin kai da gina kyakkyawar al’umma.

Kokarin dawo da darasin Tarihi a baya

Tun shekarar 2018, gwamnatin Muhammadu Buhari ta umarci dawo da darasin Tarihi a tsarin karatun firamare da sakandare a fadin ƙasa.

Tsohon ministan ilimi, Adamu Adamu, ya bayyana cewa hukumar NERDC za ta tsara sabon kundin karatu wanda zai raba Tarihi daga darasin Zamantakewa.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya fadawa gwamnonin Najeriya a Lagos, ya ba su shawara

Jaridar The Sun ta wallafa cewa tun a wancan lokacin aka shirya daukar malaman Tarihi da wasu shirye shirye amma ba a tabbatar da hakan ba.

Tinubu zai kafa kamfani a 2025

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce shugaba Bola Tinubu zai kafa wani kamfani domin rage radadi rayuwa a shekarar 2025.

Bola Tinubu ya bayyana cewa kamfanin zai yi hadaka da wasu ma'aikatun gwamnati kuma yana cikin matakan rage tsadar rayuwa da ya dauka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng