Muhimman Abubuwa 3 da 'Yan Najeriya Za Su So Ganin Karshensu a 2025

Muhimman Abubuwa 3 da 'Yan Najeriya Za Su So Ganin Karshensu a 2025

Shekarar 2024 ta bar baya da kura yayin da za a cigaba da mayar da hankali a kan wasu muhimman abubuwan a 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yau Laraba aka shiga shekarar 2025 a duniya kuma za a cigaba da fuskantar muhimman abubuwa da suka shafi siyasa, tattali da sauransu.

Akwai abubuwa da dama da suka shafi sarauta, siyasa, tsaro da sauransu da 2024 ta zo da su amma har shekarar ta kare ba a ga karshensu ba.

Sanusi
Rikicin sarautar Kano zai cigaba da jan hankali a 2025. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwan da suka ja hankali a 2024 kuma al'umma suna zuba ido su ga yadda za su kare a 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Rikicin sarautar Kano

Yadda rikicin sarautar Kano ya faro

Sarautar Kano ta fara daukar hankali tun bayan zaben 2023, inda aka fara hasashen gwamnatin Abba Kabir za ta sake tsara al'amuran masarautar, kuma ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe 'yan bindiga 40, aka kama miyagu 916 a jihar Katsina

Hakan ya haifar da sabani tsakanin masarauta da gwamnatin Kano, musamman dangane da batun gyara ko rusa masarautun da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.

Bugu da kari, ana hasashen cewa tsohon gwamna Ganduje kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya kasance mai fafutikar kare martabar matakan da ya dauka a lokacinsa.

Cigaba da shari'ar masarautar Kano a 2025

A shekarar 2025, ana sa ran za a ci gaba da fafatawa a kotu tsakanin bangarorin biyu, inda ake sa ran za a yanke hukunci game da sahihancin dokokin da suka shafi masarautun.

Ana ganin hukuncin zai iya zama mabuɗin warware rikicin ko kuma karin rikici idan wani bangare bai amince ba.

Abba Kabir
Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Ganduje. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa|Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

Haka zalika, ana hasashen shiga tsakani daga manyan dattawan Arewa da masu fada a ji, musamman ganin yadda rikicin ya shafi zaman lafiyar jihar da al'adun gargajiya.

Kara karanta wannan

An kara karya farashin fetur, za a sayar da litar mai a N400

Rikicin da ya dauki hankali a shekarar 2024, na iya zama darasi ga sauran jihohi, musamman kan muhimmancin tsarin mulki da adalci wajen tafiyar da al’amuran gargajiya da siyasa.

2. Hadakar 'yan adawa domin doke APC

Maganar hadakar PDP da Kwankwaso

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta bayyana aniyarta ta dawo da tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda yanzu haka ke jagorantar NNPP.

Shugaban PDP ya yi watsi da kalaman Kwankwaso na cewa PDP ta mutu, inda ya ce jam’iyyar har yanzu tana nan daram a fadin kasar nan.

Yiwuwar hadin kan jam’iyyun adawa

Duk da kalamansa masu tsauri kan PDP, an bayyana cewa Kwankwaso yana da damar taka muhimmiyar rawa wajen fuskantar APC a 2025.

Daily Trust ta rahoto cewa shugaban PDP ya tabbatar da cewa za su yi kokarin jawo Kwankwaso tare da hada kai da sauran jam’iyyun adawa domin kawo sauyi a siyasance.

Kara karanta wannan

Majalisa: 'Za a iya samu jinkirin amincewa da kasafin kudin 2025'

Kwankwaso
Sanata Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

A 2025, ana iya samun yunkuri na hadin kan PDP, NNPP, LP, da wasu kananan jam’iyyu domin karfafa 'yan adawa.

Kalubalen hadin kan 'yan adawa a Najeriya

Duk da yiwuwar samun daidaito, akwai kalubale masu yawa da ke iya zama cikas ga cimma hadin kan.

Wasu daga cikin su sun hada da bambance-bambancen ra’ayi tsakanin shugabannin jam’iyyun, batun fifiko, da kuma yadda za a raba mukamai idan aka yi nasara.

Shugaban PDP
Shugaban PDP, Umar Damagun. Hoto: Official PDP
Asali: Facebook

Sai dai ana ganin idan har PDP ta cimma matsaya da Kwankwaso, wannan na iya zama silar karfafa wa sauran jam’iyyun gwiwa wajen shiga cikin hadin kan.

3. Kudirin harajin Bola Tinubu

Bayani a kan kudirin haraji

Shekarar 2025 za ta kasance cike da tattaunawa kan kudirin harajin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da ya jawo ce-ce-ku-cu-ce sosai a 2024.

Punch ta rahoto cewa Tinubu ya bayyana kudirin a matsayin wani bangare na burinsa na gina kasa mai dorewa da farfado da tattali.

Kara karanta wannan

Rashin nadamar cire tallafin fetur da abubuwa 3 da Tinubu ya fada a kan manufofinsa

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A 2024, an fara tattaunawa kan kudirin, amma ra’ayoyi sun sha bamban, inda wasu ke ganin yana da matukar muhimmanci yayin da wasu ke ganin akwai bukatar kara duba shi da kyau.

Zaman majalisa kan kudirin haraji

A 2025, ana sa ran kudirin zai ci gaba da jan hankali yayin da za a cigaba da muhawara a majalisar dokoki.

Ana hasashen za a samu sabani musamman tsakanin 'yan majalisun Arewa da Kudu a kan kudirin.

Majalisa
Majalisar Dokokin Najeriya. Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

Gwamnonin Arewa sun riga sun nuna rashin gamsuwa da kudirin, suna ganin yana iya zama wata hanya ta kara jefa yankinsu cikin talauci.

Kudirin haraji: Me zai faru a karshe?

Tattaunawar kan kudirin harajin Tinubu za ta kasance cikin muhimman abubuwan da suka shafi siyasa da tattali a shekarar 2025.

Idan aka yi nasara kudirin ya samu shiga a majalisa, lamarin zai kasance babbar nasara ga mulkin Tinubu.

Kara karanta wannan

Lakurawa: Mazauna Kauyukan Sakkwato suka jawo muka jefa masu bam Inji Sojoji

Amma idan aka samu gagarumar nasara wajen dakile kudirin, za a iya fuskantar sabon yanayi na rikici a siyasar kasar nan.

Abdullahi Ganduje ya yi magana kan 2025

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai haske a 2025.

Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da cewa 'yan Najeriya za su sha jar miya a 2025 idan tsare tsaren Bola Tinubu suka fara aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng