Kamfanonin Sadarwa na Yunkurin Kara Kudin Kira, Data da Sako, Sun Bayyana Dalilai
- Kamfanonin sadarwa sun ce dole na kara kudin kira, data da SMS domin dakile matsalolin tattalin arziki da suke fuskanta
- Shugaban ALTON ya ce kamfanonin sadarwa na fuskantar durkushewa a 2025 ma damar ba a dauki matakan da suka dace ba
- Hauhawar kudin wuta da kayan aiki sun sanya kamfanonin sadarwa cikin mawuyacin hali wanda ya sa suke so ayi karin kudin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Kamfanonin sadarwa sun nemi a sake duba kudaden kira, data da SMS domin daidaita su da yanayin tattalin arziki da ake ciki yanzu.
Kamfanonin sun ce idan ba a kara kudiun ba, ba za su iya tabbatar da ingantaccen aiki ba, kuma tattalin arzikin kasar zai shiga wani mawuyacin hali.
Kamfanonin sadarwa na son kara kudin aiki
Shugaban ALTON, Injiniya Gbenga Adebayo, ya yi wannan kira a madadin dukkanin kamfanonin a wani taro a Legas, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Injiniya Adebayo ya bayyana cewa fannin sadarwa yana cikin matsala sosai, don haka ya zama dole a sake duba kudaden sabis nan take don kauce wa rushewarsu.
Ya ce idan ba a kara kudin kira, data da SMS a kan lokaci ba, burin samun ci gaba a shekarar 2025 zai zama abu mai matukar wahala.
Dalilin kamfanoni na son yin karin kudi
Injiniya Adebayo ya jaddada cewa:
“Wannan ba lokaci ba ne na jinkiri; fannin sadarwa na bukatar sababbin tsare-tsare domin ci gabansa da dorewarsa.”
Ya ce hauhawar farashin kayan aiki, karuwar kudin wutar lantarki, tsadar dala da hauhawar farashi sun haifar da babban matsin tattalin arziki ga kamfanonin sadarwa.
Shugaban ALTON ya kara da cewa, kamfanoni ba su da kudin da za su ci gaba da kula da hanyoyin sadarwa ko inganta su saboda rashin kara kudaden kira, data da SMS.
Shekara 11 ba a kara kudin sadarwa ba
A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanonin sadarwa a Najeriya, MTN, Glo, Airtel, da 9 Mobile, na duba yiwuwar ƙara kudin Data, kira, da tura saƙo.
Kamfanonin sun sanar da cewa tsawon shekara 11 ba su kara kudaden ba, duk da matsalolin sata, lalata husumiyo, da rashin wutar lantarki da ke jawo masu asara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng