Gwamnati Ta Bankado Badakalar CBN, An Gano Naira Tiriliyan 2.73 da Aka Karkatar

Gwamnati Ta Bankado Badakalar CBN, An Gano Naira Tiriliyan 2.73 da Aka Karkatar

  • Gwamnatin tarayya ta zargi CBN da karkatar da Naira tiriliyan 2.73 daga ruwan bashin buga takardun kudi domin amfanin kanta
  • Rahoton da aka bayyana ya nuna cewa CBN ta riƙe ribar wannan bashin maimakon dawo da shi cikin asusun gwamnati na CRF
  • Yayin da aka gano hakan, gwamnatin ta bukaci bankin CBN da ya gaggauta dawo mata da Naira tiriliyan 2.73 da ya kalmashe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta zargi babban bankin Najeriya (CBN) da karkatar da Naira tiriliyan 2.73 na ribar bashin Ways and Means.

Zargin ya bayyana ne a cikin bayanan kudi da aka gabatar wa majalisar dokoki ta tarayya daga babban mai binciken kudi, Shaakaar Chira.

Babban mai binciken kudi na tarayya ya bankado badakalar Naira tiriliyan 2.73 a bankin CBN
Gwamna ta gano yadda CBN ta karkatar da Naira tiriliyan 2.73 na bashin Ways and Means. Hoto: @cenbank, @MBuhari
Asali: Facebook

Ana zargin CBN da almundahanar N2.3trn

Rahoton ya nuna cewa CBN ta riƙe ribar N2.73tn daga bashin Ways and Means ba tare da mayar da ita a cikin asusun gwamnati ba, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Cire tallafi a Najeriya ya jawo wa gwamnati kabakin arziki daga bankin duniya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana cewa CBN ta yi amfani da ribar "domin amfanin bankin kawai," maimakon dawo da kudin cikin asusun kudaden gwamnati na tarayya.

Asusun gwamnatin tarayya yana da bashin N17.1tn, wanda ya haɗa da N4.4tn na bashin Ways and Means da aka bayar don magance gibin kasafi.

Dokokin da ake zargin CBN ya karya

Wannan rahoton na Shaakaar Chira ya haifar da damuwa sosai kan yadda babban bankin ke sarrafa kudaden gwamnati ba tare da bin ka'ida ba.

Tsarin mulkin Najeriya na 1999 da dokokin kudi na 2009 sun hana cire kudi daga asusun CRF ba tare da izini ba ko kuma cire fiye da yadda aka tsara.

Sashe na 80(2) na tsarin mulkin Najeriya ya ce, ba za a cire kudi daga CRF ba sai an samu izini daga hukumar da ta dace ko samun umarni na musamman.

An bukaci bankin CBN ya mayar da kudin

Kara karanta wannan

Jihohin Najeriya sun yi kasafin sama da N74trn don magance talauci a 2025

The Nation ta rahoto cewa asusun CRF da wasu hukumomi sun cire kudi fiye da yadda aka amince masu, ba tare da izini ko takardun shaida ba.

Binciken ya nuna cewa cire kudi daga asusun CRF ya haɗa da N9.41tn na bashin cikin gida da N4.45tn na Ways and Means.

An bayyana cewa CBN ta riƙe ribar N2.73tn ba bisa ƙa'ida ba, kuma an buƙaci ta mayar da wannan kuɗin cikin asusun CRF na gwamnati.

Bankin CBN ya daina ba gwamnati bashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa CBN ya sanar da daina bayar da bashin Ways and Means ga gwamnatin tarayya saboda gazawarta na biyan basussukan da ake bin ta.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce wannan matakin na daga cikin kokarin rage matsalolin kudi da gwamnati ke fuskanta wajen biyan basussuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.