NLC Ta Fadawa Tinubu Masifar da Najeriya Ta Shiga Sakamakon Cire Tallafin Fetur

NLC Ta Fadawa Tinubu Masifar da Najeriya Ta Shiga Sakamakon Cire Tallafin Fetur

  • Kungiyar kwadago ta kara jaddada cewa cire tallafin man fetur ya kawo karin matsaloli maimakon warware su a Najeriya
  • Shugaba Bola Tinubu ya kare matakin cire tallafin, yana ,mai cewa hakan ne kawai zai ceto makomar tattalin arzikin kasar nan
  • Sai dai kuma Benson Upah ya musanta furucin Tinubu, yana tambayar ko cire tallafin ya haifar wani da mai ido zuwa yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta ce cire tallafin man fetur ya haifar da karin matsaloli ga 'yan Najeriya.

Kakakin kungiyar, Benson Upah, ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani ga furucin Shugaba Bola Tinubu a hirarsa da manema labarai.

NLC ta yi martani ga kalaman Tinubu kan cire tallafin man fetur
NLC ta fadawa Tinubu illolin cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi. Hoto: @NLCHeadquarters, @officialABAT
Asali: Twitter

Tinubu ya kare matakin cire tallafin mai

A hirar, Tinubu ya ce kasar tana fuskantar barazanar rugujewa idan ba a cire tallafin man fetur ba, inda ya ce bai yi nadama ba ko kadan, a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Malamin musulunci ya bude ‘dabarar’ da ke kunshe cikin kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya ce cire tallafin ya zama dole don tabbatar da makomar tattalin arzikin kasar da na darajar kudinta.

"Muna kashe kudaden da ko samunsu ba mu yi ba. Muna kashe kudaden da ya kamata jikokinmu su mora. Ba ma zuba jari. Kawai muna yaudarar kawunanmu ne."

- A cewar Tinubu.

NLC ta yi martani ga kalaman Tinubu

Amma Benson Upah ya musanta wannan ra’ayi, yana mai cewa cire tallafin mai bai magance matsalar komai ba, maimakon haka ma sai ya haifar da karin matsaloli.

Lokacin da aka tambaye shi ko yana goyon bayan kalaman shugaban kasar, Upah ya ce, “Ba na goyon baya kuma shugaban kasar ya san gaskiyar abin da ke faruwa.”

Kakakin NNLC ya tambayi gwamnati ko cire tallafin ya magance matsalar ne, ko kuwa ya kara haifar da matsaloli da yawa fiye da a da.

NLC ta yi zanga zangar cire tallafin mai

Kara karanta wannan

Rashin nadamar cire tallafin fetur da abubuwa 3 da Tinubu ya fada a kan manufofinsa

Tun da fari, mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta gudanar da zanga zanga a fadin kasar nan domin nuna adawa da cire tallafin man fetur.

'Yan kwadagon sun zargi shugaban kasa Bola Tinubu da cire tallafin man fetur ba tare da 'gamsassun' hanyoyin rade wa al'ummar kasar radadi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.