Daga Dawowa Gida, Matasan Kano da Abba Ya Tura Karatu a Kasar Waje Sun Samu Aiki

Daga Dawowa Gida, Matasan Kano da Abba Ya Tura Karatu a Kasar Waje Sun Samu Aiki

  • Wasu mutanen da gwamnatin jihar Kano ta tura karatu a jami’o’in ketare sun kammala karatu sun dawo gida
  • Abba Kabir Yusuf da sauran jami’an gwamnatin Kano ne su ka tarbo su a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano
  • Gwamna Abba ya dauki wasu matasan aiki domin kawo cigaba musamman a bangaren kiwon lafiya da injiniyanci

Kano - A ranar Asabar, gwamnan Kano watau Abba Kabir Yusuf ya karbi mutane 150 da ya tura karatu a kasashen waje.

Gwamnatin Mai girma Abba Kabir Yusuf ta dauki dawainiyar wadannan mutane domin karo digiri a jami’o’in da ke ketare.

A Kano.
Gwamnan Kano ya ba wadanda suka je ketare aiki Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Daliban Kano sun dawo daga kasashen waje

Wani jawabi da Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafin Facebook ya ce an tarbe su ne da karfe 12:55 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit ta bibiya labarin, ta ga yadda manyan jami’an gwamnatin Kano suka tarbo daliban suka sauka a filin jirgin sama.

Kara karanta wannan

Gawurtattun ‘yan siyasa 6 da suka bar adawa, suka koma jam’iyyar APC a shekarar 2024

Gwamnatin Abba ta fitar da yara zuwa ketare

Sunusi Dawakin Tofa ya ce daliban suna cikin wadanda suka amfana da shirin kai yara karo karatu a jami’o’in duniya.

Daga cikinsu akwai mutane 150 da suka yi karatun digiri a jami’ar Sharda da wasu 98 a jami’ar Mewar duk a kasar Indiya.

Punch ta ce akwai mutane 30 da suka je jami’ar Kalinga sai wasu 29 da 23 da suka yi digirgir a jami’o’in SR da Swarnim.

Ragowar sun yi karatu a jami’ar musulunci ta kasar Uganda da aka fi sani da IUIU.

Gwamna Abba ya ba matasan Kano aiki

A wajen liyafar da aka shirya masu, Abba Yusuf ya sanar da cewa gwamnati ta dauki likitoci da kuma malaman magunguna aiki.

Sauran wadanda gwamnati ta dauki aiki sun hada da wadanda suka karatu bangarorin kiwon lafiya da kuma manyan injiniyoyi.

Gwamnan ya yabawa daliban ganin yadda suka dage su ka yi karatun da ya fitar da su waje, yake cewa yana mai alfahari da su.

Kara karanta wannan

Lakurawa: Mazauna Kauyukan Sakkwato suka jawo muka jefa masu bam Inji Sojoji

Sakon Kwankwaso ga 'yan majalisar Kano

Ku na da labari Rabiu Musa Kwankwaso ya fadawa ‘Yan majalisar tarayya abin da za su yi a kan kudirin haraji da aka bijiro da shi.

Madugun Kwankwasiyya ya ce idan ba za a kawo ayyukan alheri ba, a kyale talaka ya lallaba rayuwarsa ganin yadda ake cikin kunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng