Abba Zai Kara Tura 'Ya'yan Talakawan Kano Karatu a Manyan Jami'o'i

Abba Zai Kara Tura 'Ya'yan Talakawan Kano Karatu a Manyan Jami'o'i

  • Gwamnatin Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara kara shirin tura ƴaƴan talakawa karatu kashen ketare
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamiti mai dauke da mutane 18 da zai tantance daliban da za a zaba kafin a tura su karatun
  • Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar ya ce wasu daga cikin daliban da aka tura karatu a shekarar da ta wuce sun fara kammalawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta fara kara shirin daukar dalibai domin zuwa karatu kasashen waje.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin da zai tantance daliban jihar da za tura karatu a wannan karon.

Abba Kabir
An fara shirin daukar dalibai zuwa ketare a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Ba a gama da zargin rigima tsakaninsu ba, Kanin Kwankwaso ya maka Abba a kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba zai tura ƴan Kano karatu a jami'a

Kwamishinan ilimi mai zurfi a jihar Kano, Dr Yusuf Ibrahim Kofarmata zai jagoranci kwamitin tura dalibai karatu ketare.

Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin mutane 18 saboda zakulo talakawa masu hazaka domin a ba su tallafin karatu.

Yadda za a dauki daliban Kano zuwa waje

Dr Yusuf Ibrahim kofar mata ya bayyana cewa kwamitin zai yi gaskiya da adalci wajen ɗaukar ɗalibai da suka cancanta.

Shugaban kwamitin ya kara da cewa dalibai za su tura takardunsu wanda daga nan kuma kwamitin zai zauna ya tantance wandada suka dace.

Dr Kofarmata ya bayyana cewa kashi 40% na ɗaliban da aka tura kasashen ketare a bara sun kammala karatu.

Bayanin gwamna Abba Kabir Yusuf

Kano Focus ta wallafa cewa shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi ne ya wakilci Abba Kabir Yusuf a zaman kwamitin.

Shehu Wada Sagagi ya tabbatar da cewa babu siyasa a wajen daukar daliban kuma an kawo shirin ne domin karfafa daliban Kano masu hazaƙa.

Kara karanta wannan

Zanga Zanga: Gwamnan Kano ya ba matasan da aka tsare aikin yi bayan sun fito

Dan majalisa ya kai dalibai karatu waje

A wani rahoton, kun ji cewa dalibai 21 sun samu tallafin zuwa yin karatu a Jami'ar Fasaha ta Malaysia (UTM), za su shafe watanni 18 suna karatu a can.

An ruwaito cea dan majalisa mai wakiltar mazabar Bichi daga jihar Kano, Hon. Abubakar Kabir Bichi ne ya dauki nauyin karatun daliban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng