Gwamnan PDP Ya Ziyarci Tinubu A Legas, An Ji Abin da Suka Tattauna a cikin Bidiyo
- Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya ce an samu gagarumin ci gaba a yanayin tsaro a jihar daga Janairu zuwa Disambar 2024
- Gwamnan ya ce Shugaba Bola Tinubu ya bayar da gudunmawa sosai kuma yana da jajircewa wajen inganta tsaro a jihar
- Mutfwang ya yi wannan tsokaci ne lokacin da ya ziyarci Tinubu a gidansa da ke Bourdillon, jihar Legas, a ranar 28 ga Disamba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Gwamna Caleb Mutfwang na Filato ya bayyana ci gaban da aka samu a harkar tsaron jihar da ke Arewacin kasar nan a shekarar 2024.
Da yake magana da manema labarai bayan ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Lagos, ya danganta nasarar da kokarin jami’an tsaro, fasaha, da haɗin kan al’umma.
Gwamnan PDP ya ziyarci Tinubu
A cikin wani bidiyo da Premium Times ta wallafa, gwamnan ya ce, an yi bikin Kirsimeti cikin kwanciyar hankali a jihar Filato a 2024, saboda goyon bayan Shugaba Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin ziyarar da ya kaiwa Tinubu, gwamnan na Filato ya amince cewa ba a magance dukkanin matsaloli ba, amma akwai ci gaba mai kyau a yanayin tsaro.
Mutfwang ya tabbatar wa jama’a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tukuru don hana ayyukan ta’addanci samun wurin zama a jihar.
Gwamnan Filato ya hango nasara a 2025
Gwamnan ya bayyana kudurinsa na tabbatar da kwanciyar hankali a jihar Filato tare da ba da kwarin gwiwa ga masu zuba jari a jihar.
Gwamna Mutfwang ya samu nasarori wajen inganta tsaro a Filato, kuma gwamnan yana fatan Tinubu zai ci gaba da basu goyon baya domin samun nasarori a nan gaba.
Ya yi imani cewa shekarar 2025 za ta kasance mafi tsaro a jihar, tare da yanayi mai kyau don zuba jari da bunkasar tattalin arziki.
Kalli bidiyon a kasa:
APC ta nemi Muftwang ya fice daga PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa APC mai mulki a kasa ta fara zawarcin gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, inda take neman ya fice daga jam'iyyar adawar.
Wata kungiyar APC ta Arewa ta tsakiya ce ta yi wannan kiran a garin Jos, tana mai cewa akwai bukatar Mutfwang ya hada kai da Tinubu domin ci gaban jihar.
Asali: Legit.ng