Sojoji Sun Fadi Abin da Ya Kashe Mutane Ana Kokarin Hallaka Lakurawa a Sokoto
- Sojojin sama sun yi luguden wuta domin tarwatsa ‘yan ta’addan Lakurawa a wasu kauyuka a jihar Sokoto
- A sanadiyyar haka ne jami’an tsaron suka kashe mutanen da ba sun san hawa ba kuma ba su san sauka ba
- Kakakin Hedikwatar tsaro ya nuna cewa ba barin wutansu ne ya hallaka mutane ba, wata matsala aka samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Sokoto - Hedikwatar tsaro ta sake yin magana game da lamarin da ya faru a kauyukan jihar Sokoto har aka rasa Bayin Allah.
A wani karin haske da aka yi a ranar Juma’a, hedikwatar tsaron ta bayyana ainihin abin da ya jawo mutuwar mutane 10 a Silame.
Yadda aka rasa rayuka a Sokoto - Hedikwatar tsaro
Kamar yadda BBC ta rahoto a jiya, Darektan harkokin yada labarai na hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba ya yi karin bayani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar Edward Buba ya yi ikirarin ba bama-baman da aka jefa ne ya kashe mutane ba.
Jami’in ya bayyana cewa sojojin Najeriya sun kai hari a kan ‘yan ta’addan da ake nema, ba su aukawa mutanen da ba su da laifi ba.
Sai dai a sakamakon harin, sai aka samu fashewar wani abin a sansanin ‘yan ta’addan, wanda wannan ya jawo mutuwar mutane.
“Tabbas harin saman da aka kai ya aukawa sansanin ‘yan ta’addan wana wannan ya jawo wata fashewar dabam.
“Wadannan abin fashewa ne suka jawo rasa rayukan da aka rahoto a baya.”
- Janar Edward Buba
Buba ya kara da cewa akwai miyagun kayayyaki da makamai a wurin da wadannan ‘yan ta’adda suka fake, wannan ya kawo ajali.
Dakarun sojojin sama sun kai hari ne inda ake zargi miyagun sun boye makamai da wasu kayan aiki da taba su ya jawo tashin wuta.
Buba: 'Kayan 'yan ta'adda ya yi barna'
A jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Juma’a, ya ce asali ba luguden sojojin saman ne ya kashe wadannan mutane 10 ba.
Kafin a kai ga sakin wuta daga sama, This Day ta rahoto sojan yana bayanin binciken da aka yi domin ganin ba a hallaka marasa laifi ba.
Duk da rashin da aka yi, Janar Buba ya ce an yi nasara domin ba a yi barna sosai ba.
'Za a binciki abin da ya faru a Sokoto' - Minista
Labari ya gabata cewa Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike kan abin da ya faru a Sokoto.
Bello Matawalle na magana ne kan harin bam da sojoji suka yi kuskure da ya yi ajalin al'umma wanda ba shi ne karon farko a kasar ba.
Asali: Legit.ng