Matawalle Ya Fadi Shirinsu bayan Iftila'in Harin Bam a Sokoto, Ya ba da Gudunmawar Kudi

Matawalle Ya Fadi Shirinsu bayan Iftila'in Harin Bam a Sokoto, Ya ba da Gudunmawar Kudi

  • Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin gudanar da cikakken bincike kan harin bam din da ya kashe mutane 10 a jihar Sokoto
  • Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya kai ziyarar ta'aziyya ga Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu, tare da tabbatar da adalci kan lamarin
  • Matawalle ya ba da gudunmuwar Naira miliyan 10 ga iyalan wadanda suka mutu da wadanda ke jinya a gadon asibiti

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na gudanar da cikakken bincike kan harin bam din da ya faru ranar Laraba 25 ga watan Disambar 2024.

Harin kuskure da sojoji suka yi, ya yi ajalin mutane 10 a Gidan Bisa da Runtuwa da ke karamar hukumar Silame a jihar Sokoto.

Matawalle ya sha alwashin daukar mataki kan harin bam a Sokoto
Bello Matawalle ya yabawa Gwamna Ahmed Aliyu kan ƙoƙarin yaki da ta'addanci. Hoto: @honnaseerbazzah.
Asali: Twitter

Harin Sokoto: Matawalle ya sha alwashin daukar mataki

Kara karanta wannan

Gwamna Aliyu ya yi bayani kan batun jefa bama baman da sojoji suka yi a Sakkwato

Mai taimakawa Gwamnan Sokoto a bangaren sadarwa, Hon. Naseer Bazza shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle shi ya bayyana hakan yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai wa Gwamna Ahmed Aliyu a jihar Sokoto.

Matawalle ya bayyana abin da ya faru a kauyuka a matsayin abin takaici, tare da tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike don gano gaskiyar lamarin.

"Za a tabbatar da cewa an yi adalci kan wannan lamari, kuma gwamnati za ta dauki matakan da suka dace."
“Dr. Aliyu shi ne kadai Gwamnan da ya nemi a kafa sansanin soja a jiharsa domin tabbatar da tsaro.”

- Bello Matawalle

Matawalle ya yabawa Gwamna Aliyu kan ta'addanci

Mutawalle ya yaba da jajircewar Gwamna Ahmed Aliyu wajen yaki da 'yan bindiga da sauran ayyukan laifi a jihar Sokoto.

Ministan ya tabbatar wa Gwamnan cewa rundunar sojoji za ta ci gaba da ba da goyon baya wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya tona yadda ya samawa 'yan jiharsa ayyukan tarayya masu yawa

Har ila yau, Mutawalle ya ba da gudunmuwar N10m ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da wadanda ke jinya a asibiti saboda harin bam din.

Sokoto: Gwamna Aliyu ya jajanta kan harin bam

A baya, kun ji cewa Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ya yi alhini bisa rasuwar mutum 10 sakamakon kuskuren sojoji a kauyukan Gidan Bisa da Runtuwa.

Ahmed Aliyu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tuntuɓi shugabannin sojoji domin gudanar da bincike da kare aukuwar haka nan gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.