Ana Jimamin Ɓatan Malami, Yan Bindiga Sun Bindige Malamin Addini, an Bukaci Addu'o'i

Ana Jimamin Ɓatan Malami, Yan Bindiga Sun Bindige Malamin Addini, an Bukaci Addu'o'i

  • Yan bindiga sun hallaka Rabaran Tobias Chukwujekwu Okonkwo bayan harin da aka kai masa a jiya Alhamis
  • Wani Fasto, Rabaran Raphael Ezeogu ya bayyana cewa an kashe marigayi Tobias tsakanin karfe 7 da 8 na dare
  • Majami'ar Katolika ta Nnewi a jihar Anambra ta roƙi mabiya su yi addu’o’i ga Tobias, tare da ta’aziyyar danginsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Majami’ar Katolika ta Nnewi a jihar Anambra ta bayyana kisan gillar da yan bindiga suka yi wa Rabaran Tobias Chukwujekwu Okonkwo.

Rabaran Okonkwo, wanda likita ne, ya rasa rayuwarsa a garin Ihiala a jiya Alhamis 26 ga watan Disambar 2024.

Yan bindiga sun yi ajalin malamin addini a Anambra
An shiga tashin hankali da yan bindiga suka hallaka babban Fasto a jihar Anambra. Hoto: Legit.
Asali: Original

An hallaka babban Fasto a Anambra

Wannan kisa ya faru ne kimanin makonni biyu bayan sace tsohon babban Faston Anglican, Rabaran Godwin Okpala, wanda har yanzu ba a same shi ba, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sheikh Sani Rijiyar Lemo ya zamo Farfesan Hadisi a Jami'ar Bayero

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren Majami'ar Nnewi, Rabaran Raphael Ezeogu, ya ce an kashe Tobias tsakanin karfe 7 da 8 na dare.

Sanarwar ta bayyana kisan a matsayin babban rashi ga al’umma, amma ta nuna tabbacin samun hukuncin Ubangiji, Punch ta tabbatar.

Muƙaman da Faston ya rike a rayuwarsa

An haifi Fasto Tobias a ranar 11 ga Agustan 1984, yayin da aka ba shi mukamin a matsayin fasto a ranar 11 ga Yuli, 2015.

Kafin rasuwarsa, yana kula da makarantar koyon aikin jinya da ungozoma da dakin gwaje-gwaje na asibitin 'Our Lady of Lourdes' da ke Ihiala.

Majami’ar Katolika ta Nnewi ta yi kira ga mabiya su yi addu’o’i da yanka ga Tobias inda ta ce za a sanar da shirye-shiryen jana’izarsa nan ba da jimawa ba.

Yan bindiga sun sace Dan Majalisa

Kun ji cewa al'umma sun shiga tashin hankali da wasu ƴan bindiga suka sace ɗan majalisar dokokin jihar Anambra, Justice Azuka a Onitsha.

Kara karanta wannan

Nadin sarki ya zama rigima da aka ba tsohon mataimakin gwamna sarauta

Wani makusancinsa ya ce har yanzu babu wani labari game da inda ɗan majalisar yake ba tun bayan sace shi a ranar Talata.

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Anambra ta ce tuni dakarunta suka bazama domin ceto shi da kamo waɗanda suka sace ɗan majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.