INEC Za Ta Lalata Fiye da Katunan Zabe Miliyan 6, Hukumar Za Ta Kawo Sabon Tsari

INEC Za Ta Lalata Fiye da Katunan Zabe Miliyan 6, Hukumar Za Ta Kawo Sabon Tsari

  • Sama da katunan zaɓe miliyan shida ne ba a karɓa ba tun shekarar 2015, wanda ya haifar da cikas ga tsarin zaɓe a Najeriya
  • INEC na shirin janye katunan zaɓen da ba a karɓa tsawon lokaci tare da gabatar da fasaha ta BVAS don tantance masu zaɓen
  • Sabon tsarin zai sauƙaƙa zaɓe, rage tsadar katunan zaɓe da magance matsalar rashin damar yin zaɓe ga marasa katin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) tana shirin janye wa da lalata katunan zaɓe waɗanda ba a karɓa ba tsawon shekaru goma.

Wannan shawarar na daga cikin shawarwari 208 da hukumar ta samar bayan nazarin zaɓen shekarar 2023 da ta yi.

Hukumar zabe ta yi magana kan lalata katunan zaben da ba a karba ba tun 2015
Ana shirin canja tsarin zabe, INEC ta sanar da cewa za ta lalata katunan zabe miliyan 6. Hoto: @inecnigeria
Asali: Facebook

INEC za ta lalata katunan zabe miliyan 6

Sama da katunan zaɓe miliyan shida ne ba a karɓa ba zuwa zaɓen 2023, ciki har da waɗanda aka fitar tun shekarar 2015 a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

"Ku kara hakuri": Sanata ya rabawa mutanen mazaɓarsa buhunan shinkafa 11,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu ruwa da tsaki sun ba da shawarar cewa INEC ta janye katunan da ba a karɓa tsawon lokaci ba, musamman na shekarar 2015.

Tsaikon karbar katunan ba wai kawai yana cika tsarin gudanar da rajista ba, har ma yana haifar da wahalar gudanar da tsarin zaɓen kasar.

Tsare-tsaren INEC kan zaben Najeriya

Duk da ƙoƙarin da hukumar zaɓe da wasu kungiyoyi suka yi don sauƙaƙa karɓar katunan zaɓen, mutane miliyan shida ba su karɓa ba har yanzu.

INEC na shirin kawar da amfani da katunan zaɓe tare da gabatar da tsarin zaɓe na zamani, ciki har da damar yin zaɓe daga ƙasashen waje.

Ana buƙatar gyara dokar zaɓe ta 2022 domin tabbatar da amfani da tsarin tantance masu zaɓe ta hanyar fasahar BVAS ba tare da katin zaɓe ba.

An gano katunan zabe a otel

A wani labarin, mun ruwaito cewa an gano daruruwan katunan zabe a cikin wani otel da ke kan titin Ago Palace, yankin Ilasamanja, karamar hukumar Ishodi Osola a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan batun jefawa mutane bama bamai a Sakkwato

Wanda ya watsa hotuna da bidiyon katunan zaben ya yi ikirarin cewa katuna na 'yan mazabar ƙaramar hukumar Ishodi/Isolo ne da har yanzu ba su karba ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.