"Wannan Lokaci ne na Hakuri," Gwamnan Legas Ya Mika Ta'aziyya ga Gwamna Namadi

"Wannan Lokaci ne na Hakuri," Gwamnan Legas Ya Mika Ta'aziyya ga Gwamna Namadi

  • Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bi sahun wasu manyan kasar nan wajen mika ta'aziyya ga gwamnan Jigawa
  • Gwamna Umar Namadi ya rasa mahaifiyarsa, Hajiya Maryama da babban dansa, AbdulWahab a cikin kwanaki biyu
  • Gwamna Sanwo Olu ya taya al'umar Jigawa alhini, tare da umartarsu su ci gaba da rike imaninsu a wannan lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa - Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya mika ta’aziyyarsa ta musamman ga takwaransa na Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa rashin da ya yi na iyalinsa guda biyu.

Babban dan gwamna Namadi, Abdulwahab Namadi, ya rasu a ranar Alhamis sakamakon hadarin mota, yayin da mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi, ta rasu a ranar Laraba rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Abba Kabir Yusuf ya yi wa gwamna ta'aziyyar rasuwar dansa

Namadi
Gwamnan Legas ya mika ta'aziyya ga gwamnan Jigawa Hoto: Umar Namadi/Babajide Sanwo Olu
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana rashe-rashen a matsayin abu mai ciwo matuka, inda ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Namadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanwo-Olu ya yi ta’aziyya ga Gwamna Namadi

Gwamna Umar Namadi ya ce babu shakka, rasuwar masoyi abu ne mai matukar zafi kuma yana da wuya a fahimta, amma dole a yi imani, dole mu karbi hukuncin Allah SWT.

Gwamna Sanwo-Olu ya kara da cewa:

“A madadin iyalina, al’ummar Jihar Legas, da gwamnatinmu, ina mika ta’aziyya ga dan uwana Gwamna Umar Namadi, matarsa, ‘yan’uwan mamatan, da daukacin iyalan Namadi bisa wannan babban rashi na Abdulwahab.”

Gwamnan Legas ya taya mazauna Jigawa jimami

Sanwo-Olu ya bukaci iyalan Namadi da al’ummar Jigawa su ci gaba da jajircewa da tsayawa daram a kan tafarkin imani a wannan lokaci mai cike da kalubale.

Ya kara da cewa;

“Muna tare da ku a cikin addu’o’inmu don samun rahamar Allah ga Hajiya Maryam da Abdulwahab Namadi.”

Kara karanta wannan

Mutuwa ta sake ratsa iyalan gwamnan Jigawa kwana 1 bayan rasuwar mahaifiyarsa

Gwamnan Jigawa ya sake rasa iyalinsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Jigawa, Umar Namadi ya sake gamuwa da jarrabawar Allah SWT bayan babban dansa, AbdulWahab Namadi ya rasa ransa a hadarin mota.

Sakataren yada labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ne ya sanar da rasuwar AbdulWahab Umar Namadi kwana guda bayan rasuwar kakarsa, Hajiya Maryam.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng