Ta Tabbata: Gwamna Ya Yi Afuwa ga Ɗan Shekara 17 da Kotu Ta Yankewa Hukuncin Kisa
- Gwamna Ademola Adeleke ya yi afuwa ga Segun Olowookere da wasu mutum 52 da kotun Osun ta yanke wa hukuncin kisa
- Rahoto ya nuna cewa kotu ta yankewa Olowookere hukuncin kisa ne saboda fashi da makami ba wai saboda ya saci kaji ba
- Gwamnann jihar ya ce shawarar kwamitin jin kai ta taimaka wajen zartar da wannan afuwar ga mutanen da aka lissafa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi afuwa ga Segun Olowookere, matashin da aka yanke wa hukuncin kisa saboda fashi da makami a 2014.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Olawale Rasheed, ya fitar ranar Alhamis, ya ce an yi afuwa ga Olowookere da abokinsa Sunday Morakinyo.

Source: Twitter
Gwamnan Osun ya yafewa dan shekara 17
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shafukan sada zumunta sun cika da labarin hukuncin kisa da aka yi wa Olowookere kan zargin satar kaji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kotun jihar Osun ta sanar da cewa ba a yanke masa hukuncin a kan satar kaji ba, an yi masu hukunci ne kan fashi da makami ciki har da farmakar gidan kaji.
Gwamnan ya bayyana cewa wasu mutum 51 ma sun samu afuwa bayan shawarwarin da kwamitin shawarwari kan jin kai na jihar ya bayar.
“A bisa shawarar kwamitin jin kai, da kuma karfin iko da kundin tsarin mulki ya bani, na bai wa mutane 53 afuwa ta musamman.”
- A cewar sanarwar.
Gwamna Adeleke ya yi wa mutane da dama afuwa
Jaridar Vanguard ta rahoto sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Ina mai sanar da cewa na yafe wa mutum 30 da aka yanke wa hukunci kan kananan laifuka sauran hukuncin da ake binsu gaba daya.”
“Akwai kuma mutum 12 da aka yanke wa hukunci kan kananan laifuka, da na bayar da cikakken afuwa gare su.”

Kara karanta wannan
Yadda aminin Turji ke tsula tsiyarsa, wasu a yankin Sokoto sun roki gwamnati alfarma
“Mutum 6 da aka yanke wa hukuncin kisa sun samu sauyin hukunci zuwa sakin kai tsaye, yayin da Ojekunle Timothy ya samu sauyin hukunci zuwa shekaru 15 a kurkuku.”
Gwamna zai yi afuwa ga Segun Olowookere
Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya ji kukan iyayen yaro dan shekara 17 da kotu ta yankewa hukuncin kisa saboda satar kaji.
Gwamna Adeleke ya umarci Antoni Janar na jihar da ya yi binciken gaggawa kan Segun Olowookere da aka yankewa hukuncin domin duba yiwuwar yi masa afuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
