Jihohin Arewacin Najeriya 5 da Suka Fi Kowa Samar da Harajin VAT a 2024

Jihohin Arewacin Najeriya 5 da Suka Fi Kowa Samar da Harajin VAT a 2024

  • An fitar da wani rahoto game da jihohin da suka fi samar da harajin VAT a Najeriya a watan Nuwambar 2024 da ta gabata
  • Rahoton ya ce jihar Lagos ce ke kan gaba da makudan kudi na biliyoyi tun a watan Agusta har zuwa Nuwambar 2024
  • Bayan Lagos, jihar Rivers ce ta biyo bayanta sai kuma Oyo a matsayi na uku kafin jihar Kano da ta fi kowa a Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wasu rahotanni sun bayyana yadda jihohin Najeriya suka kawo harajin VAT duba da hada-hadar kasuwanci da ke wakana.

Jihohin Najeriya sun samar da akalla harajin N422.32bn gaba daya a rahoton da aka fitar a watan Nuwambar 2024.

Jihohin Arewa da suka samar da harajin VAT mafi yawa a 2024
An fitar da rahoton jihohin da suka fi samar da harajin VAT a Najeriya a watan Nuwambar 2024. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dauda Iliya, AbdulRazak AbdulRahman.
Asali: Facebook

Jerin jihohi da suka samar da harajin VAT

Kara karanta wannan

Yadda hukumar EFCC ta yi farautar manyan 'yan siyasar Najeriya a shekarar 2024

TheCable ta ruwaito cewa jihar Lagos ita ce kan gaba wurin samar da harajin inda ta ba da gudunmawar N242.63bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jihohin Arewacin Najeriya kuma, jihar Kano ta samar da harajin N14.43bn a watan Agusta da Nuwambar 2024.

Legit Hausa ta leko muku jihohin Arewa da suka fi samar da harajin a watan Agusta da Nuwambar 2024 da suka gabata.

1. Jihar Kano - N14.43bn

Jihar Kano ta yi kaurin suna a bangaren bunƙasar tattalin arziki musamman ta hanyar kasuwanci a Arewacin Najeriya.

Bayan samar da mafi yawan haraji a yankin, Kano ta samu N11.37bn a watan Nuwambar 2024 da muke ciki.

Sai dai a rahoton watan Agustan 2024, jihar ta samar da kasa N5bn wacce ta zama ta farko a Arewa bayan birnin Tarayya Abuja.

Abba Kabir

2. Jihar Borno - N6.65bn

Jihar Borno ta kasance ta biyu a Arewacin Najeriya bayan jihar Kano da tafi kowa samar harajin VAT.

Kara karanta wannan

Zaratan 'yan Najeriya 50 za su je Fatakwal domin gano gaskiyar a matatar NNPCL

Jihar ta samar da harajin N6.65bn a watan Agusta da Nuwambar 2024, cewar rahoton BusinessDay.

A rahoton watan Agustan 2024, Borno ta samar da harajin VAT har N3bn inda ta kuma kasancewa ta biyu a yankin.

Babagana Zulum

3. Jihar Sokoto - N5.73bn

Jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma ta samu harajin VAT na N1.84 a watan Agustan 2024.

Sai dai a watan Nuwambar 2024, Sokoto ta yi bajinta bayan samar da harajin VAT da ya kai N3.89bn.

A watan Agustan 2024 jihar ba ta cikin jerin jihohin Arewa 10 da suka fi kawo harajin yayin da ta ba da mamaki a wannan karon.

Ahmed Aliyu Sokoto

4. Jihar Kwara - N5.46bn

A rahoton da aka fitar na jihohin Arewa da suka fi samar da harajin VAT, Kwara ita ce ta hudu, kamar yadda Tribune ta tabbatar.

Jihar Kwara ta samar da harajin N2.89bn a watan Agusta yayin da a Nuwambar 2024 ta kawo N2.57bn.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Bello Turji ya kafa sabon sansanin ta'addanci a jihar Sokoto

AbdulRazak AbdulRahman Kwara

5. Jihar Jigawa - N5.42bn

Jihar Jigawa ta samu karin harajin VAT mafi yawa idan aka kwatanta da na watan Agustan 2024 da aka fitar inda ta tashi da N1.59bn kacal.

Jigawa ba ta jerin jihohin Arewa 10 da suka fi samar da harajin a watan Agusta yayin a watan Nuwambar 2024 ta samu N3.83bn.

Umar Namadi Jigawa

Gwamnatin Tinubu za ta kara harajin VAT

A wani labarin, kun ji cewa bayan ta sha musanta cewa za ta kara VAT, gwamnatin Najeriya ta ce shirin gwamnati na kara harajin ya yi nisa.

Ministan kudi da tattalin arziki na kasa, Wale Edun shi ne ya bayyana haka a taron masu zuba hannun jari da ya gudana a Washignton DC da ke kasar Amurka.

Mista Edun ya ce Majalisar Tarayya na duba batun karin harajin, kuma ana sa ran kayan alatu za a yi wa sabon karin ba tare da taba sauran bangarori ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.