'Yan Sanda Sun Dakile Mummunan Harin 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane da Dama

'Yan Sanda Sun Dakile Mummunan Harin 'Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane da Dama

  • 'Yan sanda sun dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai kan wata motar haya a Jibia, inda suka yi kokarin sace mutane goma
  • An ceto dukkanin mutane goman da aka so dauka, amma hudu sun samu raunuka, yayin da biyu suka rasa rayukansu a asibiti
  • Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta yi bayanin artabun da aka yi da kuma matakin da ta dauka na kamo 'yan bindigar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - 'Yan bindiga sun kai hari kan wata motar haya a Kwanar Makera, titin Katsina zuwa Magama Jibia a karamar hukumar Jibia, jihar Katsina.

Harin ya faru ne a ranar 24 ga Disamba da misalin karfe 8:30 na dare, inda yan bindigar dauke da miyagun makamai suka yi yunkurin sace fasinjoji goma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace matafiya kusan 20, sun nemi a biya sama da Naira miliyan 500

Rundunar 'yan sanda ta yi magana yayin da ta dakile harin 'yan bindiga a Katsina
'Yan sanda sun kubutar da mutane 10 yayin da suka dakile harin 'yan bindiga a Katsina. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Wannan bayanin ya fito ne daga wata sanarwa da ASP Abubakar Sadi Aliyu, kakakinrundunar ‘yan sandan Katsina ya fitar a shafin rundunar na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga

Sanarwar ASP Abubakar ta ce:

"Bayan samun kiran gaggawa, DPO na Jibia ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa wurin, inda suka yi musayar wuta mai zafi da yan bindigar.
"Jami’an tsaro sun samu nasarar dakile yunkurin satar mutanen sannan sun ceto dukkanin fasinjoji goma daga hannun ‘yan bindigar.
"Amma, mutum hudu daga cikin wadanda aka ceto sun samu raunuka daga harbin bindiga, an kuma garzaya da su zuwa asibiti don samun kulawar gaggawa."

Mutane biyu sun mutu daga harbin bindiga

Sai dai sanarwar ta ce mutum biyu daga cikin wadanda suka ji rauni sun mutu a asibiti yayin da ake kokarin ceto rayukansu, lamarin da ya jefa al’umma cikin jimami.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cewa tana cigaba da kokarin kamo ‘yan bindigar da suka tsere, tare da ci gaba da bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

'Ku koyi rayuwa a haka': Tinubu ya ba yan Najeriya satar amsa kan tsadar wutar lantarki

CP Aliyu Abubakar Musa ya yabawa jaruntar jami’an tsaro, tare da yin kira ga jama’a da su rika bayar da rahoto kan duk wani abin da suke zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

Masu garkuwa sun kashe dan shekara 10

A wani labari, mun ruwaito cewa wasu miyagu da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da mutane ne sun halaka wani yaro dan shekara goma a jihar Filato.

An ce 'yan bindigar sun kashe yaron mai suna Tasi'u Abdullahi mazaunin Unguwar Rikkos, da ke Jos ta Arewa, jihar Filato bayan karbar N150,000 daga iyayensa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.