Kudin Fansa: 'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Yaro Dan Shekara 10 bayan Sun Karbi N150,000
- Masu garkuwa da mutane sun kashe Tasi’u Abdullahi mai shekara 10 a Jos ta Arewa duk da karbar N150,000 na kudin fansa
- Rahoto ya nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun saka gawar yaron a cikin buhu tare da ajiyeta a kusa da gidan iyayensa
- Ya zuwa yanzu dai an ce an kama mutum biyu da ake zargi suna da hannu a kisan gillar da ya girgiza al’ummar unguwar Rikkos
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Masu garkuwa da mutane sun yiwa wani yaro dan shekara 10, Tasi'u Abdullahi kisan gilla a unguwar Rikkos, da ke Jos ta Arewa, jihar Filato.
An bayyana cewa 'yan ta'addan sun kashe yaron ne duk da cewa iyayensa sun biya N150,000 daga kudin fansar da masu garkuwar suka nema.
An sace dan shekara 10 a Filato
Rahoton Punch ya nuna cewa an gano gawar yaron a cikin buhu a ranar Juma’a, kusa da gidansu, abin da ya girgiza al’ummar yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kawu yaron, Aliyu Muhammad, ya ce an sace Tasi’u a ranar Litinin, 16 ga Disamba, a kofar gidansu bayan an yi masa wayau.
Ya ce masu garkuwan sun kira iyayensa bayan kwana biyar, suna neman N50,000 na ciyarwa da kuma N1m a matsayin kudin fansa.
Masu garkuwa sun kashe dan shekara 10
Bayan doguwar tattaunawa, iyayen yaron sun amince za su biya N300,000, amma sun fara da biyan N150,000 ta hanyar tura kudin ta banki.
Bayan biyan kudin, wata mata ta kira iyayen ranar Juma'a, ta sanar da su cewa an kashe yaron kuma an ajiye gawarsa kusa da gidansu.
Gawar Tasi’u ta nuna alamar an shake shi, domin an ga jini ya fita daga hancinsa da bakinsa.
Rahotanni sun ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin.
Sojoji sun kashe hatsabibin dan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka "Al'jan", wani dan bindiga da ya addabi yankin Tsafe da ke jihar Zamfara.
An ce sojojin tare da hadin guiwar 'yan banga sun yiwa tawagar Al'jan kwanton bauna inda suka suka yi masu luguden harsasai tare da kashe da dama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng