Tinubu Ya Sake Yin Magana kan Cire Tallafin Mai, Ya Magantu kan Kayyade Farashi
- Shugaba Bola Tinubu ya ce babu nadama kan cire tallafin man fetur a watan Mayu 2023 da ya yi a Najeriya
- Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin ya kawo gasa a bangaren man fetur, inda farashin ya fara raguwa a yau
- Ya jaddada cewa bai aminta da kayyade farashi ba, yana mai cewa za a ci gaba da kokarin samar da isasshen fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake yin magana kan cire tallafin man fetur a Najeriya.
Bola Tinubu ya ce ba shi da wani nadama kan cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023, yana mai kare wannan matakin.
Bola Tinubu ya fadi amfanin cire tallafin mai
Tinubu ya fadi haka ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja wanda hadiminsa, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Tinubu, Najeriya ba za ta iya cigaba da tallafawa makwabtan kasashe ba, domin tallafin ya zama nauyi kan tattalin arziki.
Tinubu ya ce cire tallafin yana da muhimmanci domin an daina yaudarar kai, kuma yanzu tattalin arziki yana samun gyara sosai.
Yadda cire tallafi ya rage farashin fetur
Tinubu ya kara da cewa tun bayan cire tallafin, farashin man fetur ya fara sauka saboda gasa a cikin masana’antar, ba tare da iyaka ba.
Shugaban ya bayyana cewa ba ya goyon bayan tsarin kayyade farashi, yana mai cewa kasuwanni su ne za su tsara farashi cikin 'yanci.
Tun bayan cire tallafin, farashin mai ya tashi daga Naira 200 zuwa sama da Naira 1,000 kan kowace lita, lamarin da ya kara wahalar da talakawa.
Tinubu ya magantu kan rage Ministoci
Kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya musanta batun rage yawan ministoci a gwamnatinsa, ya ce kowane da aikin da ya rataya a wuyansa.
Majalisar zartarwa ta gwamnatin Tinubu mai kimanin ministoci 50 ita ce mafi girma da aka taɓa yi a Najeriya.
Da yake maida martani ga masu sukar yawan muƙarrabansa, Tinubu ya ce dukkansu akwai aikin da ya ba su kuma suna yin yadda ya dace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng