Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta Dira a kan 'Yan Tik Tok, Ta Yi Kakkausan Gargadi

Rundunar 'Yan Sandan Kano Ta Dira a kan 'Yan Tik Tok, Ta Yi Kakkausan Gargadi

  • Rundunar 'yan sandan Kano ta ce ba za ta amince da masu kokarin haddasa hadurra a kan titunan da ke fadin jihar ba
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce babban kuskure ne abin da wasu ke yi
  • Ya shawarci jama'ar Kano da su gaggauta kawo rahoto idan aka hango wasu sun tare hanya su ma bidiyon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Rundunar 'yan sandan Kano ta ja kunnen masu daukar bidiyo domin wallafa wa ga mabiyansu a shafukan sada zumunta da su shiga hankalinsu.

Rundunar ta ce ba za ta lamunci wasu tsirarun matasa su na shiga hakkin jama'a da sunan 'content creation' a titunan da ke jihar ba tare da kokarin jawo matsaloli ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yi martani kan zargin jawo mutuwar jama'a wajen karbar tallafin abinci

Kiyawa
Yan sandan Kano sun gargadi matasa Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: UGC

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa gargadin ta bidiyon da ya sa a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sandan Kano su ja kunnen matasa

Rundunar 'yan sandan Kano ta ce ta na sane da yadda wasu matasa masu amfani da kafafen sada zumunta ke kokarin hana jama'a samar, musamman masu hawa tituna.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce;

Rundunar 'yan sandan kasa reshen jihar Kano ta ga wadannan abubuwa da aka bijiro da su, inda wadansu matasa haka kawai ka ga sun tare titi, ko su kwanta ko su na rawa a daidai lokacin da mutane su ke tafiya a kan titin.

SP Kiyawa ya jaddada cewa wannan abu babban laifi ne da ya saba da dokokin Najeriya, kuma zai iya jefa mutum a cikin fushin hukuma.

'Yan sanda sun nemi tallafi jama'a a Kano

Kara karanta wannan

Yunwa: PDP ta alakanta turmutsitsin da ya hallaka jama'a da manufofin Tinubu

Rundunar 'yan sanda Kano ta shaida wa jama'ar Kano cewa tare hanyar babu gaira, babu dalili babban laifi ne da ya kamata su rika sa ido a kai.

Rundunar ta ce duk wanda ya ga wani ko wata sun tare da sunan daukar bidiyo, a gaggauta kawo rahoto ga jami'anta domin a yi saurin daukar mataki.

'Yan sandan Kano sun ceto mutane

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan Kano ta bankaɗo wani gida da ake ajiyar mutanen da ake shirin safararsu zuwa kasashen waje a jihar.

Shugaban hukumar NAPTIP reshen jihar, Abdullahi Balarabe ya bayyana jin dadi da godiya ga 'yan sandan bayan CSP Bala Shuaibu ya jagoranci zuwa gidan a Rijiyar Lemo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng