Kwankwaso Ya Lissafa Ayyukan Alheri da Tinubu Ya Shiryawa Jihar Kano da Arewa
- Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yaba da sadaukarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi na ci gaban jihar Kano da shiyyar Arewa
- Kwankwaso ya ce aikin titin Abuja-Kaduna-Kano, gina dam-dam lakume sama da Naira biliyan 95 zai bunkasa Kano
- Jigon na APC ya jaddada cewa hukumar raya Arewa maso Yamma za ta kawo ci gaba a Kano da Arewa bisa tsare tsaren Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Musa Iliyasu Kwankwaso, sabon daraktan kudi na hukumar HJRBDA, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa kulawarsa ga Kano da Arewa.
A cikin wata wasikar godiya da ya rubuta, Kwankwaso ya bayyana manyan ayyukan da ake gudanarwa da ke nuna jajircewar shugaban kasar wajen ci gaban Arewa.
Kwankwaso ya jinjinawa kokarin Tinubu
Jaridar The Nation ta rahoto jigon na jam'iyyar APC ya na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Yunkurin gwamnatin tarayya na kammala titin Kano-Kaduna-Abuja da aikin bututun AKK da za a kammala 2025 ya nuna kishin Tinubu ga Arewa.”
A matsayin jigo a Arewa, Kwankwaso ya jinjinawa Tinubu kan amincewa da gina hanyar Kano Northern Bypass wadda Hon. Abba Bichi ya gabatar.
Kwankwaso ya ce idan aka kammala gina wannan hanyar, za a rage matsalolin sufuri tsakanin Kano da yankin Arewa maso gabas sosai.
"Shirin da Tinubu ya yi wa Kano" - Kwankwaso
Kwankwaso ya kuma ce kafa kwamitin fasaha don duba dam-dam, musamman madatsar Challawa Gorge da ta Tiga, zai bunkasa aikin noman rani a Kano.
A cewarsa, ware Naira biliyan 95 don gyaran dam-dam a Kano, wanda Sanata Kawu Sumaila ya samu, zai inganta yankin kudu na jihar.
Sannan sabuwar hukumar bunkasa Arewa maso Yamma, wacce aka kafa da goyon bayan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, za ta kawo ci gaban Arewa.
Kwankwaso ya yi godiya da samun mukami
Kwankwaso ya ce wadannan ayyukan sun tabbatar da kulawar gwamnatin Tinubu ga mutanen Kano da Arewa maso Yamma baki daya.
Ya kara da cewa:
“Manufar Renewed Hope na gwamnatin Tinubu ta fito mana a fili ta fuskar wadannan ci gaban. da Kano da Arewa suka samu'”
Yayin godiya ga nadinsa, Kwankwaso ya ce:
“Ni da iyalina da al’ummar Kano muna gode wa shugaban kasa Tinubu saboda wannan damar da aka bani na aiki a hukumar HJRBDA.”
Tinubu ya ba Kwankwaso, Bichi mukamai
Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya gwangwaje Musa Iliyasu Kwankwaso da mukamin daraktan gudanarwar kuɗi a hukumar HJRBDA.
Hukumar raya kogunan Hadejia-Jama'are (HJRBDA) ita ce ke kula da kogunan Kano, Jigawa da Buachi, wacce Musa Kwankwaso ya samu mukami a ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng