Dubu Ta Cika: An Kama Wani Malamin Addini da Ke Taimakawa Ƴan Bindiga a Zamfara

Dubu Ta Cika: An Kama Wani Malamin Addini da Ke Taimakawa Ƴan Bindiga a Zamfara

  • Kungiyar 'yan banga ta cafke malamin addini mai suna Alhaji Labbo Illela bisa zargin taimakawa 'yan bindiga a Zamfara
  • Malamin ya ce ya dade yana taimaka wa shugabannin 'yan bindiga ta hanyar tsafe makamansu da addu'o'in neman sa'a
  • Alhaji Labbo ya ce ya shafe shekara shida yana aiki da 'yan bindigar, ciki har da Sani Gurgu da ke addabar Zamfara da Katsina

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Kungiyar 'yan banga a jihar Zamfara sun cafke wani malamin addini dan shekara 75 bia zargin yana taimakawa 'yan bindiga.

An ce 'yan bangar sun cafke malamin mai suna Alhaji Labbo Illela ne bayan samun rahoto cewa shi ne ke taimakawa 'yan bindigar da magungunan sihiri.

Malamin addini da aka kama ya yi bayanin yadda yake taimakawa 'yan bindigar Zamfara
Zamfara: An cafke malamin addini da ke taimakawa 'yan bindiga da neman sa'a. Hoto: Legit.ng Hausa
Asali: Original

Mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Zagazola Makama ne ya fitar da wannan rahotona shafisa na X a ranar 22 ga Disambar 2024.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Bello Turji ya kafa sabon sansanin ta'addanci a jihar Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama malamin 'yan bindiga a Zamfara

An ga ya wallafa wani bidiyo da ke nuna dattijon malamin yayin da yake amsa tambayoyi daga 'yan bangar da suka kama shi.

An rahoto cewa malamin ya dade ya na ba 'yan bindigar kariya ta hanyar yi masu tsafi idan za su fita aiki da kuma tsafe makamansu domin samun nasara.

'Yan bangar sun mika wanda ake zargin ga jami'an tsaro domin ci gaba da bincike.

Malamin da aka kama ya yi magana

A cikin wannan bidiyo, malamin ya amsa laifinsa inda ya ce yana taimakawa shugabannin 'yan bindiga ne ta hanyar tsafe makamansu da kuma yi masu addu'ar neman sa'a.

Alhaji Labbo Illela ya ce:

"Na yarda ni malamin barayi ne na daji. Tsawon shekara shida ina tare da 'yan bindiga, kuma wadanda nake yiwa aiki mutum tara ne."

Daga cikin wadanda malamin ya taimaka mawa akwai uban daba Sani Gurgu da ke Safana, wanda yake ta'addanci a garuruwan Zamfara da Katsina.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun cafke 'yan tawayen kasar waje da suka shigo jihar Arewa

Kalli bidiyon a kasa:

'Yan bindiga sun sace malamin addini

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun sace wani babban malamin addinin Kirista a jihar Oyo yayin da suka tare motar haya.

An ce malamin na cikin motar ne a hanyarsa ta zuwa jana'iza lokacin da 'yan bindigar suka tare motar da yake ciki tare da yin awon gaba da fasinjojin ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.