Manyan Masu ba Bello Turji Kayan Yaki Sun Shiga Hannu, Za a Gurfanar da Su
- Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da wasu mutane biyar da ake zargin suna da alaka da babban dan ta'adda, Bello Turji
- Ana zargin su da samar da kayayyakin yaki da kayan more rayuwa ga 'yan ta'adda a jihohin Zamfara, Sokoto da Kaduna
- Rahotanni sun nuna cewa za a gurfanar da su a gaban Mai Shari'a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a yau
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da wasu mutum biyar da ake zargi da laifukan ta'addanci da aka ce suna da alaka da shugaban 'yan ta'adda, Bello Turji.
Ana sa ran za a gurfanar wadanda ake zargin ne a kan laifuffukan da ake tuhumarsu da aikatawa a a wasu jihohin Arewa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, an shirya gurfanar da su ne ranar Juma’a, amma ba a samu lauyan da zai wakilce su ba a lokacin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda ake zargi da taimakon Bello Turji
The Guardian ta wallafa cewa ofishin Antoni Janar na Tarayya zai gurfanar da Musa Kamarawa, Abubakar Hashimu, Bashir Abdullahi, Samuel Chinedu da Lucky Chukwuma.
An ruwaio cewa Bello Turji, Aminu Muhammad da Sani Lawal suna cikin jerin wadanda ake zargi a shari'ar duk da cewa ba su shiga hannu ba.
Laifuffukan da ake zarginsu da aikatawa
Ana zargin wadanda ake tuhuma da samar da haramtattun kayayyaki , ciki har da tabar wiwi da wasu kayan maye, abinci kayan gini da sauransu ga Bello Turji da sauran 'yan ta'adda.
Haka zalika ana zargin sun saye motar yaki daga Libya a kan kudi Naira miliyan 28.5 kuma suka kai ta ga wani shugaban 'yan ta’adda mai suna Kachalla Halilu.
Yadda suka taimaki Bello Turji a daji
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu daga cikin wadanda ake zargin sun rika ba da magunguna da mafaka domin kula da raunukan da Bello Turji ya samu yayin wani hari da ya kai.
Ana zargin sun taimaka masa ne bayan ya jagoranci kai hari kan Tungar Kolo a karamar hukumar Zurmi.
Bincike ya nuna cewa sun karya dokar hana ta'addanci ta shekarar 2013 kuma hukuncin dokar zai hau kansu idan aka same su da laifi.
Gwamna Dikko Radda ya yabawa sojoji
A wani rahoton, ku ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya yi jinjina ga sojoji kan sakin wuta da suka yi ga 'yan ta'adda.
An ruwaito cewa sojoji sun kai zafafan hare hare kan 'yan bindiga ta sama da kasa inda suka kashe miyagu da dama ciki har da Manore da Lalbi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng