Abin da Atiku Ya Ce kan Tarin Mutanen da Suka Mutu a Wajen Karbar Tallafin Abinci

Abin da Atiku Ya Ce kan Tarin Mutanen da Suka Mutu a Wajen Karbar Tallafin Abinci

  • Atiku Abubakar ya nuna alhininsa kan mutuwar tarin mutane a turmutsitsin da ya faru a Abuja da jihohin Anambra da Oyo
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana wannan iftila'in da ya faru a matsayin wani abu da ba zai manta ba da shi ba
  • Ya bukaci masu shirya tarurruka da su dauki matakan tsaro wajen gudanar da tarukansu domin kare lafiya da rayukan jama'a

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana bakin cikinsa kan turmutsitsin da suka yi ajalin mutane da jikkatar wasu a Najeriya.

Turmutsitsin da ya faru ne a Okija (Anambra), Maitama (Abuja), da Ibadan (jihar Oyo), ya jefa jama’a cikin bakin ciki mai tsanani na rashin 'yan uwansu.

Atiku Abubakar ya yi magana kan turmutsitsin da ya halaka mutane da dama a jihohin Najeria
Atiku Abubakar ya nuna alhini kan mutuwar mutane da dama a turmutsitsin karbar tallafi. Hoto: @atiku
Asali: Getty Images

Atiku ya yi alhinin mutuwar mutane

Kara karanta wannan

Adadin mutanen da suka mutu a turereniyar karbar shinkafar sadaka ya karu zuwa 22

A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar da daddare a shafinsa na X, Atiku ya bayyana lamarin a matsayin "abin tausayi" tare da nuna damuwa kan mutuwar mutanen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abukabar ya ce:

“Cike da nauyin zuciya na karbi labarin wannan rashin mutane a turmutsitsin da suka faru a Okija da Abuja, wanda ya jawo mutuwar mutane da dama."

Ya kara da cewa:

"Wannan alhini ya kara tsananta bayan mutuwar yara fiye da 30 a Ibadan, yayin wani taron shakatawa a jihar Oyo."

Atiku ya nemi tsaurara tsaro a tarukan jama'a

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da jajantawa gwamnatocin jihohin da abin ya shafa.

The Guardian ta rahoto Atiku ya jajantawa wa Cocin Katolika, musamman Holy Trinity Catholic Church da ke Maitama, inda daya daga cikin turmutsitsin ya faru.

Atiku ya yi kira da a kara daukar matakan tsaro wajen gudanar da manyan taruka don tabbatar da tsaron lafiyar mahalarta irin wadannan taruka.

Kara karanta wannan

Bayan faruwar iftila'i a Najeriya, Tinubu ya soke bukukuwan da ya shirya, ya jajanta

Mutanen da suka mutu a Anamba sun kai 22

A wani labarin, mun ruwaito cewa mutanen da suka mutu a turmutsitsin karbar tallafin shinkafar Kirsimeti a jihar Anambra ya haura zuwa 22.

Rundunar 'yan sandan Anambra ta sanar da cewa mutane da dama sun jikkata kuma suna kwance a asibiti yayin da ake gudanar da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.