Kimanin mutane 20 sun mutu sakamakon 'turereniya' a Coci

Kimanin mutane 20 sun mutu sakamakon 'turereniya' a Coci

A kalla mutane ashirin ne suka mutu, wasu da dama suka samu raunuka, sakamakon cunkuson jama'ar da ya haifar da 'turereniya' a wata Coci da ke gabashin kasar Tanzania, kamar yadda wani jami'in gwamnati ya sanar ranar Lahadi.

Cocin ta yi amfani da wani babban filin wasa domin gudanar da harkokin ibada da yammacin ranar Asabar a garin Moshi da ke daura da tsaunin 'Kilimanjaro'.

Yayin turereniyar da ta barke a daidai lokacin da za a fara raba wani 'mai' mai tsarki, mambobin Cocin sun tattake 'yan uwansu marasa karfi da kananun yara da mata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 20 tare da raunata wasu da dama.

"Mutane 20 sun mutu yayin da wasu 16 suka samu raunuka yayin hatsarin, biyar daga cikin wadanda suka mutu kananan yara ne. Turereniya ta bare a wurin ne yayin da masu bauta a Cocin suka fara rige - rigen karbar wani 'mai' mai tsarki," a cewar jami'in gwamnati, Warioba.

Babban limamin Cocin, Fastp Boniface Mwamposa, ya yi kaurin suna a kasar Tanzania wajen tara dandazon mabiya Cocinsa domin basu maganin cututtuka da kuma fahamin samun nasara a rayuwa da lakanin tsare kai daga miyagu, aljanu da shaidanu.

Kimanin mutane 20 sun mutu sakamakon 'turereniya' a Coci
Kimanin mutane 20 sun mutu sakamakon 'turereniya' a Coci
Asali: Twitter

Mahukunta a kasar sun nuna cewa mai yiwuwa adadin mutanen da suka mutu ya karu saboda yawan mutanen da suka halarci filin wasan da kuma la'akari da cewa lamarin ya faru ne a lokacin da gari ya fara yin duhu.

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya tona asirin cin amanar da Ganduje da Abdullahi Abbas suka yi wa jam'iyyar a Kano

"Akwai yiwuwar adadin mutanen da suka mutu zai karu saboda lamarin ya faru ne da daddare. Har yanzu muna bincike a kan lamarin," kamar yadda Warioba ya bayyana.

Ana samun karuwar limaman Coci da ke ikirarin mu'ujiza da yi wa magoya bayansu alkawuran fitar da su daga kangin talauci da basu nasara a harkokinsu na rayuwa.

Dubban mutane ne ke halartar Cocin Pentecostal a kasar Tanzania mai mutane miliyan 55. Cocina, a duk inda suke a fadin duniya, suna samun kudin shiga ne daga karbar haraji da kyauta daga mambobinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel