‘Abin da Tinubu Ya Fada Mana game da Ta’addanci a 2025’: Matawalle Ya Magantu

‘Abin da Tinubu Ya Fada Mana game da Ta’addanci a 2025’: Matawalle Ya Magantu

  • Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya fadi umarnin da shugaban kasa, Bola Tinubu ya ba su kan ayyukan ta'addanci
  • Ministan ya ce Tinubu ya ba umarnin kawo karshen yan ta'addan da ayyukansu a shekarar 2025 da za a shiga
  • Matawalle ya kuma nuna damuwa kan yadda ta'addanci ya ki karewa inda ya zargi ma su ba su bayanai da laifi kan haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba sojojin Najeriya umarni kan ayyukan ta'addanci.

Tinubu ya umarce su da su tabbatar da cewa an kawo karshen ta'addancin 'yan bindiga a shekarar 2025.

Bello Matawalle ya fadi umarnin Tinubu kan ayyukan ta'addanci
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ce Bola Tinubu ya umarce su da su kawo karshen ta'addanci a 2025. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Dr. Bello Matawalle.
Asali: Facebook

Matawalle ya fadi shirin sojoji kan ta'addanci

Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle shi ya bayyana hakan a ranar Asabar 21 ga watan Disambar 2024, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Kakakin Majalisa ya fadi abin da ya faru kan kwace filinsa, ya gargadi hukumar FCTA

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matawalle ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar APC a gidansa da ke Gusau a jihar Zamfara.

Ministan ya tabbatar da cewa sojojin za su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun cika umarnin shugaban kasa, Daily Post ta ruwaito.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta kammala shirye-shirye domin tura karin sojoji da kayan aiki zuwa wuraren da rikici ya fi tsananta a yankin Arewa maso Yamma.

'Wadanda ke kawo cikas a yakar ta'addanci' - Matawalle

“Gwamnatin Tarayya da manyan hafsoshin soji suna cikin damuwa matuka kan batun masu ba ‘yan bindiga bayanai.
“Wannan shi ne babban kalubalen da ya hana nasara akan yaki da ‘yan bindiga."

- Bello Matawalle

Matawalle ya koka cewa masu ba ‘yan bindiga bayanai inda ya ce suna daga cikin al’ummar yankunan da suke sayar da imaninsu domin neman kudi.

Zuwan Lakurawa ya dagula ran manyan yan bindiga

Kara karanta wannan

Bayan faruwar iftila'i a Najeriya, Tinubu ya soke bukukuwan da ya shirya, ya jajanta

A wani labarin, kun ji cewa shugabannin yan bindiga da dama sun shiga tsaka mai wuya bayan bullar yan kungiyar Lakurawa.

An tabbatar da cewa Lakurawa na neman kwace ikonsu tare da bukatar su shiga tafiyarsu ta kafa daular Musulunci.

Daga cikin wadanda ke tsaka mai wuya akwai manyan yan bindiga, Dogo Gide da Najaja wadanda ke fargabar za a kwace ikonsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.