Dubu Ta Cika: Sojojin Najeriya Sun Cafke Wasu Manyan Masu Safarar Makamai a Arewa
- Dakarun OPSH sun cafke masu safarar makamai biyu a Filato a lokacin da suke shirin siyan bindigar Naira miliyan 1.45
- An kama Kenneth Mayas da Bulus Yilfo daga Forop, tare da ƙwato Naira miliyan 1.45 daga hannunsu a cikin wani hotel
- Sojoji sun fara gudanar da bincike kan waɗanda ake zargin, yayin da jami’ai ke ci gaba da neman sauran 'yan ƙungiyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Dakarun Operation Safe Haven (OPSH) sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da safarar makamai a Bokkos, jihar Filato.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kama wadanda ake zargin, Kenneth Mayas, mai shekaru 31, da Bulus Yilfo, mai shekaru 60
Zagazola Makama, wani mai sharhi kan lamuran tsaro a Najeriya ne ya fitar da wannan rahoto a shafinsa na X a ranar Juma'a. 20 ga Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Filato: An cafke masu safarar makamai
Makama ya ce an cafke mutanen ne a mabuyarsu da ke a otel ɗin White House ranar Juma’a yayin da suke ƙoƙarin siyan bindigar AK-47 a kan Naira miliyan 1.45.
Dukkannin wadanda aka kama, sun fito ne daga garin Forop da ke a karamar hukumar Barkin Ladi, jihar Filato.
Dakarun sun ƙwato kuɗi har Naira miliyan 1.45 daga hannun waɗanda ake zargin, waɗanda ake tunanin suna cikin wata babbar ƙungiyar ɓarayi.
Ana gudanar da bincike kan miyagun
Dakarun sun ce waɗanda ake zargin da da aka kamata tare da kuɗaɗen da aka ƙwato suna hannun jami’ai yanzu haka don gudanar da bincike.
Ana ci gaba da gudanar da aiki don kama sauran mambobin ƙungiyar ɓarayin.
Wannan aiki ya nuna himmar dakarun sojin Najeriya wajen kawar da aikata laifuffukan da suka shafi safarar makamai a Filato da kewaye.
An cafke masu sayarwa 'yan bindiga makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Najeriya sun yi nasarar cafke wasu ake dake zargin suna safarar makamai ga 'yan bindiga a Kaduna da Filato.
Mai magana da yawun rundunar soji da ke atisayen OPSH, Manjo Samson Zhakom ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Jos, jihar Filato.
Asali: Legit.ng