'Hakan Ya Zama Dole': Shugaban Kamfanin BUA Ya Yabawa Tsare Tsaren Tinubu, Ya Jero Dalilai
- Fitaccen dan kasuwa a Najeriya kuma shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ya yabawa salon mulkin Bola Tinubu
- Abdulsamad ya ce tabbas matakan da shugaban ke dauka suna da tsauri amma hakan shi ne kaɗai mafita
- Hakan na zuwa ne yayin da ake korafi kan matakan shugaban da suka jefa al'umma cikin kunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ya yabawa tsare-tsaren Bola Tinubu a Najeriya.
Mai kamfanin BUA ya yaba da gyare-gyaren tattalin arziki da Tinubu ya aiwatar inda ya ce matakin suna da wahala amma yana tafiya a hanya madaidaiciya.
Abdulsamad BUA ya yabawa tsare-tsaren Tinubu
Abdulsamad Rabiu ya fadi hakan ne a yau Juma’a 20 ga watan Disambar 2024 yayin da ya kai ziyarar ban girma ga Tinubu a Lagos, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shahararren dan kasuwar ya amince cewa gyare-gyaren suna da zafi, amma ya ce suna da matukar muhimmanci.
“Ko da yake mun san cewa wasu daga cikin gyare-gyaren da mai girma shugaban kasa ya aiwatar suna da wahala, ya zama dole a yi su.
“Gaskiya ne cewa wasu daga cikinsu suna da matukar wahala, amma muna bukatar wadannan gyare-gyaren, musamman hadin kai da aka yi a fannin canjin kudi na kasashen waje.”
- Abdussamad Rabiu
Yadda Tinubu ya dauki matakan gyara tattalin arziki
Baya ga cire tallafin man fetur, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya aiwatar da tsarin hade dukkan bangarorin kasuwar canjin kudade.
Hakan yana daga wani bangare na kokarin samar da gaskiya a kasuwanni da kuma karfafa kwarin gwiwar masu zuba jari, The Nation ta ruwaito.
Duk da cewa an yaba da wannan manufar a matsayin mai kyau kuma wajibi, ta kara matsa lamba kan kudin kasar da masana’antu, tare da haifar da karin tsadar kayayyaki.
Siminti: Dangote, BUA za su samu kishiya
Kun ji cewa wani babban kamfanin China ya saye gaba daya hannayen jarin Holcim da ke a kamfanin simintin Lafarge Afrika a kan $838.8m.
Lafarge na daya daga cikin manyan kamfanonin siminti da kayan gini a Najeriya, watakila tafiyar Holcim za ta iya canja farashi.
Asali: Legit.ng