Sojoji Sun Sha Yabo kan Kashe Gagga Gaggan 'Yan Bindiga, Manore da Lalbi

Sojoji Sun Sha Yabo kan Kashe Gagga Gaggan 'Yan Bindiga, Manore da Lalbi

  • Gwamnatin Jihar Katsina ta yaba da haɗin gwiwar sojojin sama da na kasa wajen kawar da sansanonin ƴan bindiga a tsaunin Bichi
  • Rahotanni sun nuna cewa sojoji sun samu nasarar kashe wasu gagga-gaggan ƴan bindiga da dama ciki har da Manore da Lalbi
  • Gwamnatin Katsina ta ce nasarar sojojin Najeriya ta taimaka wajen rage barazanar ƴan bindiga a yankunan Danmusa, Safana, da Kankara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina – Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana godiya ga rundunar Operation FANSAN YAMMA da sojojin runduna ta 17 bisa ragargazar 'yan bindiga.

Rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin sun samu nasarar kai wani gagarumin farmaki a sansanonin ƴan bindiga a tsaunin Bichi.

Sojoji
Sojoji sun hallaka manyan 'yan bindiga a Katsina. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Hadimin gwamnan Katsina ya wallafa a Facebook cewa an kai farmakin ne a ranar 19 ga Disamba, 2024.

Kara karanta wannan

Dogo Gide, Najaja sun shiga matsi da bullar Lakurawa, ana hasashen dagulewar lamura

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Dr Nasir Muazu, ya ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da kafa sansanonin ƴan bindiga a tsaunin Bichi.

Yadda sojoji suka farmaki 'yan bindiga

Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigar sun yi kaurin suna wajen satar mutane, kwacen shanu, da kai hare-hare a ƙauyuka kamar Maidabino, Yantumaki, da Danmusa.

Matukan jiragen yaki na rundunar sojojin sama sun yi amfani da makaman zamani wajen lalata sansanonin ƴan bindigar tare da kai hare-hare kan wuraren da suka ɓuya.

Jirgin sama
Jirgin sojojin saman Najeriya. Hoto: Nigerian Air Force HQ
Asali: Twitter

Ƴan bindigar da suka tsira sun yi ƙoƙarin taruwa amma sojojin ƙasa suka afka musa tare da yin musayar wuta mai tsanani.

Bayan shan wuta daga sojoji, wasu daga cikin su sun tsere da babura amma jiragen yaki suka sake bin sawunsu tare da kai musu hari a sabon wurin da suka taru.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke masu jigilar makamai, sun kwato tarin makamai

An yabawa sojoji bisa kashe 'yan bindiga

Gwamnatin Katsina ta yaba wa rundunar Operation FANSAN YAMMA da dakarun runduna 17 bisa wannan gagarumin nasara da suka cimma.

Dr. Nasir Muazu ya jaddada cewa nasarar alama ta jajircewar sojoji wajen dawo da zaman lafiya a jihar Katsina da kewaye.

'Yan bindiga sun gwabza fada a tsakaninsu

A wani rahoton, kun ji cewa an tafka fada mai zafi tsakanin wasu shugabannin 'yan ta'adda a yankin Safana na jihar Katsina.

Rahotanni sun tabbatar da cewa fadan ya jawo mutuwar wasu manyan shugabannin 'yan bindiga uku da suka shahara da ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng