Yadda Tinubu, Shettima Za Su Kashe Sama da N9bn a Tafiye Tafiye da Abinci a 2025

Yadda Tinubu, Shettima Za Su Kashe Sama da N9bn a Tafiye Tafiye da Abinci a 2025

  • Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima za su kashe Naira biliyan 9.36 a kan tafiye-tafiye, kayan makulashe da abinci a 2025
  • An ware Naira biliyan 6.14 don tafiye-tafiyen waje na Tinubu, yayin da Shettima zai kashe biliyan 1.31 kan irin wannan tafiyar
  • Idan mu ka waiwaya 2024, Tinubu da Shettima sun kashe sama da Naira biliyan 5.24 kan tafiye-tafiye tsakanin Janairu da Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima za su kashe Naira biliyan 9.36 a tafiye-tafiye da cin abinci a 2025.

Alkaluman sun fito ne daga bayanan kasafin kudi na 2025 da ma’aikatar tsare-tsare da kasafin kudi ta fitar.

Tinubu, Shettima za su lakume biliyoyin Naira a tafiye tafiye da abinci a 2025
Tinubu, Shettima za su kashe sama da biliyan 9 a tafiye tafiye da abinci a 2025. Hoto: @PBATMediaCentre
Source: Twitter

Abinci da tafiye tafiyen Tinubu, Shettima a 2025

Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin Naira tiriliyan 49.7 ga majalisar dokoki ta kasa a ranar Laraba a cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Wani ciyaman ya bi sahun gwamnoni, ya gabatar da kasafin biliyoyi a 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi wa kasafin kudin 2025 taken: "Kasafin gyara, tsaron zaman lafiya da samar da ci gaba."

A cewar takardar kasafin, Tinubu zai kashe Naira biliyan 7.44 a tafiye-tafiye da kayan makulashe, yayin da Shettima zai kashe Naira biliyan 1.9 a kan hakan.

Yadda Tinubu, Shettima za su lakume N9.36bn

Tafiye-tafiyen kasashen waje na Tinubu a 2025 za su ci Naira biliyan 6.14, yayin da na cikin gida za su ci Naira miliyan 873.9.

Har ila yau, an ware Naira miliyan 431.6 don kayan makulashe, abinci da kayan girki na shugaba Tinubu.

Tafiye-tafiyen kasashen waje na Shettima a 2025 za su lakume Naira biliyan 1.31, yayin da na gida za su ci Naira miliyan 417.5.

Kayan makulashe, abinci da kayan girki na Shettima za su ci Naira miliyan 186.02, kamar yadda yake kunshe a kasafin na 2025.

Nawa shugaba Tinubu ya kashe a 2024?

Kara karanta wannan

ACHR: "Tinubu ya yi wani abin da tsofaffin shugabannin Najeriya suka gagara yi"

A 2024, Tinubu, Shettima, da uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu sun kashe akalla Naira biliyan 5.24 kan tafiye-tafiye tsakanin Janairu zuwa Maris.

Wannan ya fito ne daga bayanan GovSpend, wani dandalin fasaha da ke bin diddigin yadda gwamnatin tarayya ke kashe kudin gudanarwarta.

Me aka warewa Tinubu, Shettima a 2024?

Idan mu ka waiwaya 2023, Legit Hausa ta rahoto cewa Bola Tinubu da Kashim Shettima sun samu Naira biliyan N15.961bn na tafiye-tafiye a kasafin kudin 2024.

Yayin da kasafin ya nuna cewa shugaban kasar da mataimakinsa za su ci abincin N5.128bn a 2024 an kuma ware N6bn domin motocin fadar shugaban kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com