Abin da Buhari Ya Ce bayan Wike Ya Kwace Filinsa da na Wasu Manya a Abuja
- Kakakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya wanke shi kan kiran sunansa da ake yi kan filaye da aka kwace a Abuja
- Garba Shehu ya musanta cewa filin na Buhari ne kai tsaye inda ya ce Gidauniya ce ta magoya bayansa suka siya masa
- Kakakin ya ce watakila yayin cika takardu ne suka saba ka'idar hukumar FCTA da har ya kai aka kwace filin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kakakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan labarin kwace filinsa a Abuja.
Garba Shehu ya yi karin haske kan rahotannin da ke cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kwace filin da aka ware wa Gidauniyar Muhammadu Buhari.
Buhari ya yi magana kan kwace filinsa
A cikin bayanin da ya yi a ranar Laraba 18 ga watan Disambar 2024, Shehu ya ce filin ba na tsohon shugaban kasar ba ne a matsayinsa na mutum daya, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai Garba Shehu ya ce an mallake shi ne domin Gidauniyar ta hanyar sahalewa da wasu abokan aikinsa suka yi da kyakkyawan niyya.
Gidauniyar wacce aka kafa ta bisa ka’ida tare da goyon bayan magoya bayan Buhari ta saba da ka'idojin Hukumar FCDA.
Hukumar ta fito da kudin takardar mallakar filin da aka bayyana a matsayin mai tsada fiye da yadda aka saba domin irin wadannan kungiyoyi.
Ko da yake ba a san dalilin da ya sa aka kwace filin ba, Shehu ya ce watakila hakan na iya zama sakamakon kuskure ko kuma wani matakin gudanarwa da aka yi da gangan.
An ja hankalin masu saka sunan Buhari
Garba Shehu ya kara da cewa Buhari, a matsayinsa na mutum daya, yana da filin da aka bashi a Abuja kafin zama shugaban kasa, Daily Post ta ruwaito.
A lokacin mulkinsa, Buhari ya ki karbar wani karin fili da aka bashi, yana mai cewa ya kamata a ba wadanda ba su da filaye a Abuja fifiko.
Shehu ya ja hankalin masu sukar lamarin da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yi hanzarin yanke hukunci inda ya gargadi masu neman shigar da sunan Buhari cikin rikice-rikicen.
Wike ya kwace filayen Buhari da wasu manya
A baya, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kwace wasu filaye guda 762 a Maitama saboda rashin biyan kuɗin takardun mallakar filayen.
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan Kaduna, Uba Sani na daga cikin wadanda Wike ya kwacewa filaye.
Asali: Legit.ng