N607bn: Majalisa Ta Yi wa Gwamna Gata, Ta Amince da Kasafin 2025 da Ya Gabatar

N607bn: Majalisa Ta Yi wa Gwamna Gata, Ta Amince da Kasafin 2025 da Ya Gabatar

  • Majalisar Anambra ta amince da kasafin kudin N607bn na 2025 da Gwamna Chukwuma Soludo ya gabatar mata a Nuwamba
  • Kakakin majalisar, Somto Udeze, ya ce aiwatar da kashi 80 na kasafin 2024 ya ba da kwarin gwiwar amincewa da kasafin 2025
  • Kasafin kudin da gwamnan ya gabatar ya kunshi N139.5bn na ayyukan yau da kullum da kuma N407.5n na manyan ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Majalisar jihar Anambra ta amince da kasafin kudin 2025 na N607bn da Gwamna Chukwuma Soludo ya gabatar a watan Nuwamba.

Majalisar ta amince da kasafin kudin ne bayan wani kuduri daga shugaban masu rinjaye, Hon. Ikenna Ofodeme.

Kakakin majalisar Anambra ya yi magana yayin amincewa da kasafin 2025 da Chukwuma Soludo ya gabatar
Majalisar Anambra ta amince da kasafin 2025 da Chukwuma Soludo ya gabatar. Hoto: @CCSoludo
Asali: Twitter

Majalisar Anambra ta amince da kasafin 2025

Kakakin majalisar, Somto Udeze, ya ce amincewa da kasafin kudin na nuna hadin kai tsakanin majalisa da bangaren zartarwar jihar, inji rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Tinubu: PDP ta tono 'illolin' da ke cikin kasafin 2025, ta gargadi majalisa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rt. Hon. Udeze ya bayyana gamsuwa da cewa an aiwatar da kasafin shekarar da ta gabata da kashi 80 cikin 100, yana fatan hakan zai ci gaba a 2025.

Kakakin majalisar ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da mara wa gwamnatin Chukwuma Soludo baya tare da biyan haraji.

Majalisa ta yi gyare-gyare a kasafin 2025

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Hon. Ejike Okechukwu, ya bayyana cewa an amince da kasafin kudin kamar yadda gwamna ya gabatar.

Duk da haka, ya ce an yi 'yan gyare-gyare a cikin kudin da aka warewa ma’aikatu da sassan gwamnati, amma adadin kudin kasafin bai canza ba.

Kasafin kudin ya kunshi kashe N139.5bn a ayyukan yau da kullum, da N407.5 a manyan ayyuka wadanda suke wakiltar kashi 23 da 77 na kasafin.

Gwamna zai yi afuwa ga masu garkuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo ya shirya yin afuwa ga masu garkuwa da mutane da ƴan fashi da makami da suka tuba.

Gwamna Chukwuma Soludo na shirin daukar wannan matakin ne a wani yunkuri na kawo karshen matsalolin tsaro da jihar Anambra ke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.