Mutuwar Yara 35: Ƴan Sanda Sun Cafke Tsohuwar Matar Wani Babban Sarki a Najeriya

Mutuwar Yara 35: Ƴan Sanda Sun Cafke Tsohuwar Matar Wani Babban Sarki a Najeriya

  • Rundunar 'yan sandan Oyo ta kama Naomi Silekunola, tsohuwar matar Ooni na Ife da wasu mutum bakwai kan mutuwar yara 35
  • An rahoto cewa yaran 35 sun gamu da ajalinsu ne a wajen wani turmutsutsun taron nishadi da aka shirya a wata makaranta a Ibadan
  • rundunar 'yan sanda ta ce ta fara binciken kisan kai, kuma sun tabbatar da cewa adalci zai samu ga iyalan da suka rasa 'ya'yansu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Rundunar 'yan sandan Oyo ta kama Naomi Silekunola, tsohuwar matar Ooni na Ife, da wasu mutum bakwai kan mutuwar yara 35 a Ibadan.

Turmutsutsun da ya jawo silar mutuwar yaran ya faru ne a ranar Laraba a makarantar Islamiyya ta Bashorun, cikin garin Ibadan.

'Yan sandan Ooyo sun yi magana yayin da suka kama tsohuwar matar sarkin Ife
'Yan sanda sun kama tsohuwar matar sarkin Ife yayin da yara 35 suka mutu a Oyo. Hoto: @Ooni_of_Ife
Asali: Twitter

'Yan sanda na binciken mutuwar yara 35

Kara karanta wannan

Ana tuhumar tsohuwar matar sarki kan mutuwar yara 32 a makarantar Musulunci

Jaridar The Cable ta rahoto cewa an shirya taron ne karkashin gidauniyar Wings, da nufin yara 5,000 su halarta amma adadin ya haura 7,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, Osifeso Adewale, mai magana da yawun 'yan sanda na jihar Oyo, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu yara 35 sun rasu.

Osifeso ya ƙara da cewa Fasasi Abdulahi, shugaban makarantar da aka yi taron, yana daga cikin wadanda aka kama kan wannan lamarin.

Rundunar 'yan sandan ta ce ta tura lamarin zuwa sashen binciken kisan kai na rundunar da ke a Iyaganku kuma mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar ke jagorantar binciken.

'Yan sanda sun kama matar sarkin Ife

Sanarwar kakakin 'yan sandan ta ce:

"Bari in sanar da al'ummar jihar cewa an kama mutum 8 daga cikin wadanda suke da hannu a wannan mummunan al'amari"
"Wadanda aka kama sun hada da Naomi Silekunola, Fasasi Abdulahi, Genesis Christopher, Tanimowo Moruf, Anisolaja Olabode, Idowu Ibrahim da Abiola Oluwatimilehin.

Kara karanta wannan

Fafaroma ya fadi yadda ya tsallake harin kunar bakin wake sau 2 a kasar Iraqi

"A halin yanzu, yara 35 sun mutu, yayin da 6 suka samu munanan raunuka."

Rundunar ta kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalan da abin ya shafa kuma ta tabbatar da cewa za a yi adalci a binciken wannan mummunan al'amari da ya faru.

Mutane 31 sun mutu a wajen rabon abinci

A wani labarin, mun ruwaito cewa akalla mutane 31 sun gamu da ajalinsu a wajen rabon abinci a wani cocin Kings Assembly da ke Fatakwal, jihar Ribas.

An rahoto cewa dandazon mutane ne suka halarci taron rabon abinci, lamarin da ya jawo turmutsutsu a wajen shiga dakin da ake rabon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.