Kotu Ta Rataye Masu Garkuwan da Suka Sace Sarki Suka Kashe Shi
- Kotun Jihar Delta ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan mutane uku bisa laifin garkuwa da kisan sarkin gargajiya
- An yankewa daya daga cikin wandanda aka samu da laifin hukuncin shekaru 14 a gidan yari bisa amfani dukiyar marigayin ba bisa ka’ida ba
- Shaidun masu gabatar da kara sun hada da Fasto Charles Afamefuna Ugboh, wanda aka yi garkuwa da shi tare da sarkin amma ya tsira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - Kotun Jihar Delta ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum uku da aka samu da laifin kisan sarkin Ubulu-uku, Obi Edward Akaelue Ofulue III.
Alkalin kotun, Mai Shari’a M. Omovie, ta tabbatar da cewa masu shigar da kara sun gabatar da hujjoji da suka tabbatar da laifuffukan wadanda aka tuhuma.
Rahoton Leadership ya nuna cewa bayan kisan kai, an tuhumi wadanda aka kama da tarin laifuffuka a gaban kotun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lafin matasan da suka kashe sarki
Masu garkuwan da aka yankewa hukuncin kisa sune Suleiman Musa, Umar Mohammed, da Garba Abubakar Haruna wanda aka fi sani da Dogo.
An tuhume su da aikata laifuffukan garkuwa da mutane, hadin baki domin yin garkuwa, fashi da makami, da kuma kisan marigayi sarkin Ubulu-uku.
Matasan sun aikata laifuffukan ne a ranar 6 ga watan Janairu, 2016, inda suka yi garkuwa da sarkin tare da Fasto Charles Afamefuna Ugboh a kan titin Obior.
Yadda shaidu suka yi bayani ga kotu
Masu gabatar da kara daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Delta, karkashin jagorancin Anthony Orhorhoro, sun gabatar da shaidu biyar domin tabbatar da zarge-zargen su.
Daya daga cikin shaidun, Fasto Charles Afamefuna Ugboh, ya bayar da shaidar yadda aka yi garkuwa da shi tare da sarkin, da yadda ya samu tsira daga hannun wadanda ake tuhuma.
Kotu za ta rataye masu garkuwa a Delta
The Nation ta wallafa cewa bayan nazarin hujjoji, Mai Shari’a Omovie ta bayyana cewa an tabbatar da laifukan wadanda ake tuhuma ba tare da shakka ba,..
Daga nan kuma ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da yanke hukuncin shekaru 14 a gidan yari ga Jemilu Ahmed bisa samun dukiyar sarkin a hannunsa.
Yara 32 sun rasu a makarantar jihar Oyo
A wani rahoton, kun ji cewa ana cigaba da bincike kan sanadiyyar mutuwar yara 32 a wata makarantar Musulunci a jihar Oyo.
Rahotanni sun nuna cewa gwamna Seyi Makinde ya tattabar da cewa za a hukunta duk wanda aka samu da hannu wajen jawo kisan yaran.
Asali: Legit.ng