Sanata Abdul Ningi Ya Buga Muhawara da Akpabio a Majalisar Dattawa
- Sanata Abdul Ningi ya kalubalanci dalilin da yasa gwamnonin jihohi ba sa amfani da kudin da ake ba su kan tsaro yadda ya kamata
- Abdul Ningi ya nemi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi bayani a kan lamarin kasancewarsa tsohon gwamna
- Sanata Akpabio ya yi bayani kuma ya soki kafafen yada labarai bisa zargin mayar da hankali kan munanan labarai a mafi yawan lokuta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da tsohon Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye, Sanata Abdul Ningi sun yi muhawara a majalisa.
Muhawarar ta biyo bayan wata tattaunawa ne kan kudurin gaggawa da Sanata Anthony Siyako Yaro na PDP daga Gombe ya gabatar kan hare-haren 'yan bindiga a jiharsa.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Sanata Abdul Ningi ya nuna takaici ne kan yadda ake ba gwamnoni kudi a kan tsaro amma kuma a cewarsa ba a gani a kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tambayar Sanata Ningi ga Akpabio
Sanata mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP, Abdul Ningi ya tambayi dalilin da ya sa gwamnonin ba sa amfani da kudaden tsaro don magance matsalolin jihohinsu.
Abdul Ningi ya ce dokar kasa ta bayyana cewa gwamnonin jihohi su ne shugabannin tsaro a jihohinsu, don haka suna da alhakin kare rayuka da dukiyoyi.
TV Plantinium ta wallafa biyon Ningi yana cewa kowanne gwamna yana karbar sama da Naira miliyan 500 a matsayin kudin tsaro duk wata amma ba a gani a kasa sosai.
Martanin Akpabio ga Sanata Abdul Ningi
Da yake mayar da martani, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Akpabio ya ce sai lokacin da Abdul Ningi ya zama gwamna zai gane yadda ake amfani da kudin.
Ya kara da cewa yawancin nasarorin tsaro da ake samu ba sa zuwa kafafen watsa labarai saboda galibi kafafen labarai sun fi son munanan labarai.
Akpabio ya bayyana cewa tsaro aiki ne na kowa da kowa kuma gwamnonin jihohi ba za su iya barin aikin tsaro ga gwamnatin tarayya kadai ba.
Adadin garkuwa da aka yi a shekara 1
A wani rahoton, kun ji cewa Cibiyar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar da rahoto kan yadda aka yi garkuwa da mutane a Najeriya a shekara daya.
Rahoton NBS ya nuna cewa an sace mutane sama da miliyan 2 tare da karbar kudin fansa sama da Naira tiriliyan 2 a jihohin Najeriya.
Asali: Legit.ng