Matakan da Gwamnonin Arewa Suka Hadu Suka Dauka na Murkushe 'Yan Bindiga
- Rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa ya nuna an biya har Naira tiriliyan N2.23 a matsayin kudin fansa tsakanin Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024.
- Yankin Arewa maso Yamma ya fi fuskantar yawan garkuwa da mutane, inda aka sami rahoton laifuffukan sace mutane har miliyan 14.4
- Jihohin da ke Arewa sun fara daukar matakan tsaro na gida tare da hada kai da kungiyoyin sa-kai da farar hula domin magance matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Wani rahoto daga Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun biya kudin fansa da ya kai Naira tiriliyan N2.23, daga 2023 zuwa 2024.
Yankin Arewa maso Yamma ya fi fuskantar irin wadannan matsaloli, inda aka samu rahoton laifuffuka garkuwa miliyan 14.4.
Jaridar Punch ta hada rahoto a kan yadda gwamnonin Arewa suka fara daukar matakin samar da tsaro wajen amfani da 'yan banga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakan tsaro da jihohi suka dauka
Jihohi da dama a Arewa sun fara daukar matakan tsaro na gida domin taimaka wa kokarin Gwamnatin Tarayya wajen yakar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
A Kano, gwamnatin jihar ta dauki 'yan sa-kai 2,500 domin inganta tsaro, inda ake horar da su a Cibiyar Horaswa ta Tsaro ta Jihar da ke Gabasawa.
A jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar da 'yan sa-kai 3,969 domin dakile matsalolin rashin tsaro da ke addabar jihar.
Haka zalika, gwamnatin jihar Kogi ta dauki ma’aikata 3,000 daga kungiyoyin sa-kai da fararen hula domin tabbatar da tsaro a kananan hukumomi 21 a jihar cikin shekara guda.
Matakan da aka dauka a Bauchi da Kebbi
A jihar Bauchi, gwamnatin jihar na amfani da kungiyoyin sa-kai da aka yi wa rajista bisa doka domin yakar matsalolin ‘yan bindiga da ta’addanci.
A Sokoto, an kafa dakarun Community Guard Corps domin tallafa wa jami’an tsaro tare da ba su bayanai masu amfani.
Hakazalika, a jihar Kebbi, gwamnatin ta yi alkawarin ba wa kungiyoyin sa-kai tallafi na kudade domin karfafa aikinsu na taimaka wa jami’an tsaro.
Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya dauki matakin samar da 'yan sa-kai da ba su makamai domin yakar 'yan bindiga.
An kama 'yan daba a jihar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi babban kamu yayin da ta kama tarin 'yan daba.
ASP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa rundunar ta kama 'yan dabar ne yayin da ta kai samame wasu unguwannin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng