Yadda NNPCL Ya Karbo Rancen Dala Biliyan 1 domin Tallafawa Matatar Man Dangote

Yadda NNPCL Ya Karbo Rancen Dala Biliyan 1 domin Tallafawa Matatar Man Dangote

  • NNPCL ya karbo bashin dala biliyan 1 domin tallafawa aikin matatar Dangote a lokacin da matatar ta shiga wata matsala ta kudi
  • Sake bude matatar Fatakwal wani ci gaba ne mai muhimmanci da ya nuna jajircewar NNPCL kan samun wadatar makamashi
  • An rahoto cewa Mele Kyari ya jagoranci sauye-sauye a NNPCL, wanda ya kai ga samun riba a karon farko cikin shekaru masu yawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin man Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta karbo rancen dala biliyan 1 domin tallafawa aikin matatar Dangote.

Shugaban watsa labaran kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Abuja.

NNPCL ya yi magana kan nasarorin da kamfanin ya samu karkashin shugabancin Kyari
NNPCL ya sanar da cewa ya karbo bashin dala biliyan 1 domin taimakawa matatar Dangote. Hoto: @nnpclimited
Asali: Facebook

Soneye ya sanar da cewa NNPCL ta kai ga nasarori masu yawa a bangaren man fetur da iskar gas karkashin shugabancin Mele Kyari, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya dawo da zancen kudirin haraji, ya cigaba da lallabar jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarorin NNPCL karkashin Mele Kyari

Jami'in ya ce sake farfado da matatar mai ta Fatakwal babban ci gaba ne a kokarin Najeriya na kaiwa ga wadatar makamashi a cikin gida.

NNPCL ta dauki tsarin amfani da gas din CNG domin samarwa ‘yan Najeriya makamashi mai tsafta da arha a kokarin da gwamnati ke yi na rage dogaro da fetur.

NNPCL a karkashin shugabancin Mele Kyari, Soneye ya sanar da cewa:

"A wata nasara da shiga cikin tarihi, NNPC, karkashin jagorancin Kyari, ta samu riba a karon farko cikin shekaru da dama, wanda ke nuna gagarumin sauyi.
"Tuni dai kamfanin ya zarce adadin ribar da ya kiyasta zai samu a shekarar 2024, lamarin da ke nuni da sauye-sauyen da Kyari ya aiwatar sun haifar da da mai ido."

NNPCL ya tarbo bashin $1bn saboda Dangote

Olufemi Soneye ya kuma bayyana cewa:

“NNPCL ya karbo lamunin $1bn domin tallafawa matatar Dangote a lokacin da take fama da matsalar kudi, wanda ya share fagen kafa matatar mai ta farko mai zaman kanta a Najeriya."

Kara karanta wannan

Kama tsofaffin gwamnoni, ministoci da manyan nasarorin EFCC da ICPC a shekarar 2024

Wannan matakin a cewar Soneye ya nuna jajircewar NNPCL wajen bunkasa hadin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu domin ci gaban kasar nan.

Har ila yau, Sonoye ya ce Kyari ya samu damar karbo bashin dala biliyan 3 wanda ya taimaka wajen daidaita darajar Naira a lokacin matsin tattalin arziki.

An samu sabani tsakanin Dangote da NNPCL

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa an samu sabani tsakanin kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) da matatar man Dangote da ke jihar Legas.

A yayin da Dangote ya ce NNPCL ya yi dakon lita miliyan 111 na fetur daga matatarsa, shi kuma NNPCL ya dage cewa lita miliyan 16.8 kadai matatar ke iya fitarwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel