Majalisa Ta Gaji da Walagigin Naira, Ta Gabatar da Kudirin Hana Amfani da Kudin Ketare

Majalisa Ta Gaji da Walagigin Naira, Ta Gabatar da Kudirin Hana Amfani da Kudin Ketare

  • Yayin da darajar Naira ke kara karyewa a Najeriya, Majalisar Dattawa ta dauki mataki domin dakile hakan
  • Majalisar tarayyar ta gabatar da kudirin ne domin hana amfani da kudin kasashen waje wurin cinikayya
  • Hakan ya biyo bayan kokarin da bankin CBN ke yi na ganin an farfaɗo da darajar kudin a Najeriya da aka karya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT Abuja - Majalisar Dattawa a Najeriya ta dauki mataki domin dawo da martabar darajar Naira.

Majalisar ta gabatar da dokar hana amfani da kudaden kasashen waje da hada-hadarsu a Najeriya.

Majalisa ta gabatar da kudiri domin bunkasa darajar Naira
Majalisar Dattawa ta gabatar da kudirin hana amfani da cinikayya na kudin ketare a Najeriya. Hoto: The Senate.
Asali: Facebook

Majalisa ta shirya farfaɗo da darajar Naira

Daily Trust ta ruwaito cewa Majalisar tarayyar ta yi hakan ne da nufin hana cinikayya da kudaden domin bunkasa darajar Naira.

Kara karanta wannan

Majalisa ta amince a kashe biliyoyi a gina tashoshin lantarki a Sokoto da wasu garuruwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gabatar da wannan kudirin ne domin tabbatar da cewa duk wata cinikayya ciki har da albashi, za a rika biyan su ne da Naira a kasar.

Dokar tana kuma da nufin karfafa gwiwa ga amfani da Naira, domin kawo karshen nuna wariya kan darajarta a cikin gida.

Sanata Ned Munir Nwoko shi ya gabatar da kudirin a Majalisar Dattawa domin farfaɗo da darajar Naira a Najeriya da ma ketare, cewar Daily Post.

Muhimmancin kudirin da aka gabatar a Majalisar

Dan Majalisar ya gabatar da kudirin mai taken: “Kudirin sauya dokar babban bankin Najeriya na 2007, lamba 7, domin hana amfani da kudaden ketare domin biyan kuɗi da sauran abubuwan da suka danganci hakan,” domin inganta Naira.

Sanata Nwoko ya ce amincewa da Dalar Amurka da Fam na Ingila da Yuro a matsayin kudin cinikayya na cikin gida, na nufin cigaba da karfafa tasirin tsarin mulkin mallaka,

Kara karanta wannan

An samu matsala, Tinubu ya dakatar da gabatar da kasafin kudin 2025

Darajar Naira ta sake faduwa a kasuwa

Kun ji cewa a karo na biyu a jere, Dalar Amurka ta kara tashi a kasuwar canji ta bayan fage ranar Alhamis, 12 ga watan Disambar 2024.

Bayanai sun nuna cewa darajar Naira ta sauka zuwa N1,668 daga farashin da aka yi cinikin kowace Dala kan N1,600 a ranar Laraba 11 ga watan Disambar 2024.

Sai dai kuma a ɗaya ɓangaren darajar kudin Najeriya ta farfaɗo a kasuwar gwamnati, inda Dala ta rikito zuwa N1,534.6.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.