Ba Ganduje ba ne: Kwankwaso Ya Fadi Mutum 1 da Yake Haddasa Matsala a Jihar Kano
- Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi ikirarin Rabiu Musa Kwankwaso ne babbar matsalar siyasar Kano, ba Abdullahi Ganduje ba
- Tsohon kwamishinan ya ce Kwankwaso bai dauki Ganduje da mutanensa a bakin komai ba, yayin da ya gabatar da wasu hujjoji
- Musa Iliyasu Kwankwaso ya kara da cewa jam'iyyar NNPP ta ja layi tsakaninta da wasu 'yan siyasa tun bayan cin zaben Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hon. Musa Iiyasu Kwankwaso ya yi ikirarin cewa ba tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne matsalar jihar ba.
Tsohon kwamishinan raya karkara, ya ce Sanata Rabiu Musa Kwanwaso, jagoran jam'iyyar NNPP ne babbar matsalar jihar Kano.

Source: Twitter
'Rabiu Kwankwaso ne matsalar Kano' - Musa Iliyasu
A wata hira da rediyon Express Kano, Hon. Musa Iliyasu ya gabatar da wasu hujjoji da ya ce sun isa su gamsar da jama'a cewa Kwankwaso ne matsalar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon kwamishinan ya ce:
"Ba Ganduje ne matsalar siyasar Kano ba, Kwankwaso ne babbar matsalar domin ina da da kwararon hujjoji a kai."
Hon. Musa Iliyasu ya ce wannan ra'ayin nasa kusan shi ne ra'ayin duk wani mai bibiyar siyasar Kano, duk da cewa wasu na ganin matsalar ta Ganduje ce.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kare ikirarinsa
Da aka tambaye shi dalilansa na cewa Kwankwaso ne matsalar Kano ba Ganduje ba, Musa Iliyasu ya shaida cewa:
"Akwai lokacin da kanin Kwankwaso ya rasu, Ganduje ya je ta'aziyya gidan iyaye da hakimin Kwankwaso, kuma mun je har gidansa mun yi masa ta'aziyya.
"Haka mutuwar hakimi, Ganduje na Dubai amma ya tura tawaga, aka je jana'iza, kuma ya tura tawaga karkashin Dakta Gawuna, aka je yi wa Kwankwaso ta'aziyya.
"Abin takaici, mahaifiyar matar Ganduje, Dakta Hafsat ta rasu, Kwankwaso na gari, bai je ba, kuma ya hana mutanensa su je yana cewa makiyi ne."

Kara karanta wannan
Ana shirin ballowa tsohon gwamna ruwa, ya yi barazana ga masu son hada shi da Tinubu
NNPP ta ja layi da wasu 'yan siyasa
Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma yi ikirarin cewa tun bayan da jam'iyyar NNPP ta ci zabe a Kano ta ja layi tsakaninta da wasu 'yan siyasar jihar.
"Ai tun da aka ci zabe, da Kawu Sumaila, Kofa, Kabiru Alasan, Sani Madakin Gini, aka ja layi da su, kuma Kabiru ya fadi hakan a gidan rediyo."
Tsohon kwamishinan ya ce akwai bukatar Kwankwaso ya daidaita da Ganduje, yayin da yake buga kirji da cewa APC ce za ta karbi mulki a zabe mai zuwa.
Kalli cikakkiyar hirar a nan kasa:
Ganduje ya ki zuwa auren 'yar Kwankwaso
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ki halartar daurin auren 'yar jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
An ce wannan ramuwar gayya ce Ganduje ya yi kan kin zuwa auren 'yarsa da Kwankwaso ya yi a shekarar 2018, lokacin yana matsayin gwamnan Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
