'Babban Hatsari ne Cewa sai Mulkin Najeriya Ya Koma Arewa a Zaben 2027'

'Babban Hatsari ne Cewa sai Mulkin Najeriya Ya Koma Arewa a Zaben 2027'

  • Tsohon hadimin Goodluck Jonathan ya gargadi yan Arewa game da zaben 2027 da lalata siyasarsu gaba daya
  • Reno Omokri ya ce masu neman sai mulkin Najeriya ya dawo Arewa a 2027 suna neman kawo cikas ne a kasa
  • Ya musanta maganar da ake cewa Arewa sun shafe shekaru 11 ne kacal a kan mulkin Najeriya inda ya fayyace komai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon hadimin Goodluck Jonathan mai suna Reno Omokri ya magantu kan zaben 2027.

Omokri ya ce kiran da ake yi mulki ya koma yankin Arewacin Najeriya a 2027 babban hatsari ne.

Reno Omokri ya gargadi yan Arewa kan mulkin Najeriya a 2027
Reno Omokri ya lissafa yawan shekaru da kowane yanki ya mulki Najeriya. Hoto: Reno Omokri.
Asali: Facebook

Omokri ya fadi lokacin da dimukraɗiyya ta dawo

Omokri ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a shafinsa na X a jiya Litinin 16 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ji tausayin 'yan Najeriya, ya amince matafiya su hau jirgi kyauta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wadanda ke kiran dawo da mulki yan siyasa ne da ke cewa Arewa ta mulki Najeriya na shekaru 11 tun 1999.

Sai dai Omokri ya ce ba 1999 ba ne aka dawo mulkin dimukraɗiyya a Najeriya inda ya ce Arewa ta fi Kudu mulkar kasar.

Shekarun Arewa da Kudu a mulkin Najeriya

Reno Omokri ya ce a shekaru 64 bayan samun yancin kai, Arewa ta yi mulkin shekaru 46 yayin da Kudu ke da 18.

"Idan ka kasafta mulkin kasar a dimukraɗiyya, Arewa ta yi mulkin shekaru 21 dai kuma Kudancin Najeriya ta yi shekaru 14."
"Abubakar Tafawa Balewa ya yi shekaru shida sai Shehu Shagari yana da hudu, Umaru Musa Yar'adua shekaru uku sai kuma Muhammadu Buhari shekaru takwas."
"A Kudancin Najeriya kuma Obasanjo ya yi shekaru takwas sai Goodluck Jonathan mai shekaru biyar sannan Tinubu da ke kan mulki yana kasa da shekaru biyu."

Kara karanta wannan

'Yadda aka yi wa Buhari dabaibayi, aka hana shi sakat a shekaru 8,' Dalung

- Reno Omokri

Omokri ya gargadi Arewa ka da ta dauki matakin da zai kawo mata cikas a siyasarta.

Omokri ya soki masu murnar faduwar Naira

Kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya soki ƴan Najeriya da ba su fata mai kyau ga cigaban darajar Naira a kasuwa.

Omokri ya bayyana haka ne a lokacin da darajar Naira ta jera kwanaki biyu ta na samun karuwa a kasuwar musayar kuɗaɗe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.