Bello Turji Ya Yi Barazana da Aka Cafke Babban Abokinsa, Ya Gindaya Sharadi
- Bayan jami'an tsaro sun yi nasarar cafke dan ta'adda, Bago Wurgi, shugaban yan bindiga, Bello Turji ya yi martani
- Bello Turji ya yi barazanar daukar munanan matakai na kai hare-hare a wasu yankunan da ke Sokoto da Zamfara
- Rahotanni sun ce Turji zai iya yin komai tun daga ba da dukiyarsa zuwa kai hare-hare idan ba a sako Wurgi ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Sokoto - Hatsabibin dan fashin daji, Bello Turji ya yi barazana bayan cafke babban abokinsa, Bako Wurgi
An bayyana cewa Bello Turji ya yi barazanar ɗaukar matakai masu tsauri bayan cafke wani dan ta'adda, Wurgi.

Asali: Facebook
Turji ya fusata da cafke abonkinsa, Wurji
Rahoton Zagazola Makama ya ce Wurgi yana a matsayin babban abokinsa kuma mai muhimmin matsayi wajen tattaunawa da karɓar kudin fansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yana kula da yankunan gabashin Sokoto musamman daga garuruwan Isa, Sabon Birni da kuma Shinkafi a Zamfara.
Majiyoyi na sirri sun tabbatar cewa cafke Wurgi ya fusata Turji ƙwarai, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin al'ummar yankunan da kuma hukumomi.
An tabbatar Bello Turji ya riga ya tuntuɓi manyan sarakuna da shugabannin al'umma, ya yi barazanar kai munanan hare-hare idan ba a sako Wurgi ba.
Alwashin da Turji ya yi kan kama Wurgi
A wani ɓangaren kuma, Turji ya yi ikirarin cewa zai kashe dukiya mai yawa ko yawan dabbobi domin ganin an sako Wurgi.
Ana hasashen cewa yana da adadi mai yawa na dabbobi kuma ya bayyana aniyar amfani da su domin tilasta hukumomi su sako abokinsa, cewar Daily Post.
Duk da haka, idan ƙoƙarinsa bai cimma nasara ba, Turji zai ɗauki matakai masu tsanani da kawo tashin hankali a yankunan gabashin Sokoto da Shinkafi.

Kara karanta wannan
Ana shirin ballowa tsohon gwamna ruwa, ya yi barazana ga masu son hada shi da Tinubu
Har ila yau, Turji ya yi barazanar kashe wasu daga cikin waɗanda yake garkuwa da su, musamman mazauna Isa da Sabon Birni da Shinkafi.
An yi arangama da yan banga, yaran Turji
Kun ji cewa mun samu rahotanni cewa kazamar fada ta barke tsakanin 'yan banga da kuma wasu yaran Bello Turji.
An yi arangamar a yankin Fadamar Tara da ke jihar Zamfara inda yan ta'addan suka yi kokarin kwace iko a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng