Tinubu Ya Ji Tausayin 'Yan Najeriya, Ya Amince Matafiya Su Hau Jirgi Kyauta

Tinubu Ya Ji Tausayin 'Yan Najeriya, Ya Amince Matafiya Su Hau Jirgi Kyauta

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince 'yan Najeriya su hau jirgin kasa kyauta daga ranar 20 ga watan Disamba 20 zuwa 5 ga Janairu
  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya dauki wannan matakin ne domin tallafawa masu karamin karfi a kasar
  • Idan za a tuna, an yi rin wannan garabasar a bara yayin bikin Kirsimeti da Sallah, shi ne Tinubu ya amince da sake yi a bana

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince 'yan Najeriya su hau jiragen kasa kyauta a fadin kasar nan daga 20 ga Disamba, 2024 zuwa 5 ga Janairu, 2025.

Wannan mataki na daga cikin hanyoyin da aka dauka don rage nauyin kudin sufuri yayin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Gwamnati ta sanar da janye karbar kudi ga matafiyan da za su hau jirgin kasa a fadin kasar
Gwamnatin Tinubu ta ayyana zirga zirgar jiragen kasa kyauta ga 'yan Najeriya. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Tinubu ya amince a hau jirgin kasa kyauta

Kara karanta wannan

An samu matsala, Tinubu ya dakatar da gabatar da kasafin kudin 2025

Ministan sadarwa da bunkasa al’adu, Mohammed Idris, ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban kasa, da ke Abuja, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya bayar da wannan umarni yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda ya jagoranta a ranar Litinin, 16 ga Disamba.

Dakta Mohammed Idris ya sanar da cewa:

“Kamar yadda muka yi a bara, za a samar da zirga-zirgar jirgin kasa kyauta daga 20 ga Disamba zuwa 5 ga Janairu.”

Dalilin Tinubu na daukar wannan mataki

Jaridar Punch ta rahoto ministan sadarwar ya kara da cewa:

“Wannan mataki na nuni da burin shugaban kasa na rage nauyin sufuri, musamman ga masu karamin karfi a kasar nan.”
“A bara an yi irin wannan lokacin bikin Kirsimeti da Sallar Layya, kuma Shugaba Tinubu ya sake amincewa da hakan a wannan shekarar.”

An rahoto cewa nan gaba kadan ne gwamnatin tarayyar za ta ayyana ranakun hutun Kirsimeti tare da na sabuwar shekara kamar yadda aka saba.

Kara karanta wannan

'Arewa na fushi da kai': an gargadi Tinubu ya gyara tafiyarsa, yankin na neman mafita

An yafe kudin jirgin kasa ga matafiya

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya amince matafiya su hau jirgin kasa kyauta daga tashar jirgin Fatakwal zuwa tashar Aba.

Gwamnatin tarayya ta ce Tinubu ya dauki wannan mataki ne domin ganin cewa matafiya a tsakanin garuruwan biyu sun samu saukin sufuri na kwanaki hudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.