Gwamnatin Tarayya Ta Canja Sunan Jami'ar Abuja, An Karrama Tsohon Shugaban Kasa

Gwamnatin Tarayya Ta Canja Sunan Jami'ar Abuja, An Karrama Tsohon Shugaban Kasa

  • Gwamnatin tarayya ta sauya sunan Jami’ar Abuja zuwa Jami’ar Yakubu Gowon domin girmama tsohon shugaban kasar
  • Ministan sadarwa ya ce wannan shawara ta fito ne daga taron FEC da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban kasa
  • Za a tura bukatar sauya sunan jami'ar ga majalisar tarayya domin tabbatar da canjin wanda zai zama alamar tunawa da Gowon

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da sauya sunan jami’ar Abuja, inda yanzu za a rika kiranta da sunan jami’ar Yakubu Gowon.

Ministan sadarwa da bukasa al’adu, Mohammed Idris, ya bayyana wannan mataki ga manema labarai a fadar shugaban kasa ranar Litinin.

Ministan sadarwa ya yi magana yayin da ake shirin canja sunan jami'ar Abuja
Gwamnatin tarayya ta sauyawa jami'ar Abuja suna zuwa jami'ar Yakubu Gowon.
Asali: Twitter

Gwamnatin Tinubu ta karrama Yakubu Gowon

An cimma wannan shawarar ne a taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) wanda shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, a cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Ana neman Obasanjo, IBB, Buhari, Jonathan su hadu, su kifar da Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sauya sunan jami'ar da nufin girmama tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon, wanda kwanan nan ya cika shekara 90 da haihuwa.

Idris ya ce za a mika shawarar canja sunan jami'ar ga majalisar tarayya domin samun amincewa.

Takaitaccen bayani game da jami'ar Abuja

An kafa jami’ar Abuja da ake kira da Uni Abuja, a watan Janairu na shekarar 1988 karkashin dokar ta 110 ta 1992 (da aka sabunta).

Channels TV ya rahoto cewa jami’ar ta fara gudanar da harkokin karatu a shekarar 1990 tare da bikin kaddamar da dalibanta na farko da ta fara dauka.

Janar Yakubu Gowon tsohon shugaban mulkin soja ne na Najeriya da ya jagoranci kasar daga shekarar 1966 zuwa 1975.

Jami'ar Abuja ta dauki sabon matakin koyarwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'ar Abuja ta dauki wani sabon salo na horar da dalibanta wanda zai tilasta masu mallakar kamfani kafin kammala karatu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ji tausayin 'yan Najeriya, ya amince matafiya su hau jirgi kyauta

Jami'ar ta ce mallakar kamfani zai taimakawa daliban jami'ar dogaro da kansu tare da iya daukar wasu aiki idan sun kammala makaranta ba tare da jiran gwamnati ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.