Attajirin Arewa, BUA Zai Sake Gina babban Masallacin Zazzau da Ya Rufta kan Mutane

Attajirin Arewa, BUA Zai Sake Gina babban Masallacin Zazzau da Ya Rufta kan Mutane

  • Alhaji Abdul Samad BUA ya dauki nauyin sake gina masallacin Jummah na Zazzau da ya rushe a 2023, inda ya fara bayar da N2bn
  • Sabon masallacin zai dauki mutane 7,000, sannan zai samu wuraren zamani kamar ICT, dakin karatu, a cewar Sarkin Zazzau
  • Gwamnatin Kaduna tana kokarin neman karin kudade domin ganin an kammala ginin masallacin cikin watanni 18 da aka tsara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Shugaban gidauniyar ASR Africa da BUA Group, Alhaji Abdul Samad Rabiu, ya kaddamar da sake gina masallacin Juma'a na Malam Abdulkarim da ke Zazzau.

Wadanda suka halarci bikin sun hada da gwamnan Kaduna, Uba Sani, sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli da shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas.

Sarkin Zazzau ya yi magana yayin da aka kaddamar da sake gina masallacin Zariya da ya rushe
Abdul Samad BUA ya dauki nauyin sake gina masallacin Zariya da ya rushe. Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Za a sake gina masallacin Zazzau

Masallacin mai dumbin tarihi wanda aka gina a shekarar 1836, ya rushe a ranar 11 ga Agusta, 2023, inda ya hallaka mutum bakwai, a cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An daura auren fitaccen mawakin Kannywood: Ado Gwanja, Hamisu Breaker sun halarta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rushewar masallacin ya kuma jikkata wasu da dama, wanda hakan ya sa Alhaji Abdul Samad BUA ya dauki nauyin sake gina shi.

Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamalli, ya yaba da gudunmuwar Naira biliyan biyu da Abdul Samad ya bayar da kuma sake ginin masallacin karkashin gidauniyarsa ta ASR Africa.

Sarkin Zazzau ya yabawa Abdul Samad Rabiu

Masallacin idan aka kammala ginawa, zai iya daukar mutane 2,000 a benen sama da kasa, tare da karin 5,000 a harabar masallacin, wanda aka shi a tsari na zamani.

Zanen masallacin ya nuna da cewa za a gina wurin alwala na zamani, dakin karatu, cibiyar ICT, da ofisoshin gudanarwa don amfanin al'umma.

Sarkin Zazzau ya ce rushe masallacin abu ne mai ciwo, amma ya zama dole domin tsaron rayukan masallata masu ibada.

Gwamnan Kaduna zai nemo karin kudi

Shugaban majalisar wakilai, Dr Tajudeen Abbas, ya bayyana masallacin a matsayin wani muhimmin gini na tarihi da ke wakiltar tarihin Zazzau.

Kara karanta wannan

Hotuna: Fitaccen mawakin siyasa, Rarara ya bude sabon gidan biredi a jihar Katsina

Rt. Hon. Abbas ya ce aikin gina masallacin zai dauki wata 18, inda kudin da ake da su yanzu za su isa a yi kusan kashi 50% na aikin.

Gwamnan Kaduna, Mallam Uba Sani, ya ce gwamnatin jihar tana kokarin neman karin kudade daga masu ruwa da tsaki don kammala aikin masallacin.

Tun lokacin da masallacin ya rufta a lokacin Ssallar Azahar a watan Agusta 2023, mutane suke yin kira da a gaggauta sake gina masallacin.

CAN ta jajanta kan rushewar masallacin Zariya

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yi jajen rushewar masallacin Zariya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da jikkatar wasu da dama.

Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya bayyana kaduwarsa kan lamarin, tare da isar da ta'aziyya ga iyalan mamatan da al'ummar musulmi baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.