Sarkin Musulmi Ya Jagoranci Raba Zakkar Miliyoyin Naira ga Talakawa

Sarkin Musulmi Ya Jagoranci Raba Zakkar Miliyoyin Naira ga Talakawa

  • Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi ya halarci taron shekara-shekara na Zakka da Waqafi da aka gudanar a Haɗejia
  • Taron ya samu jagorancin Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III da sauran sarakuna da manyan baƙi daga ciki da wajen Najeriya
  • An ƙaddamar da rabon Zakka a garin Lafiya a yankin Guri inda aka rarraba kayan amfanin gona da dabbobi ga mabuƙata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - A ranar Asabar, 14 ga Disamba gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya halarci taron shekara-shekara na Zakka da Waqafi da ƙungiyar AZAWON ta shirya.

Taron ya gudana a Haɗejia kuma ya mayar da hankali kan ilmantar da shugabanni da al'umma kan muhimmancin fidda Zakka da tasirin sa wajen tallafawa mabuƙata da haɓaka tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Yaki da 'yan bindiga: Manyan Arewa sun halarci kaddamar da askarawa 5,000

Sarkin Musulmi
An raba zakka a jihar Jigawa. Hoto: Garba Muhammad
Asali: Facebook

Hadimin gwamnan jihar Jigawa, Garba Muhammad ya wallafa a Facebook cewa mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa’adu Abubakar III ya halarci taron..

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Musulmi ya yabi Jigawa kan zakka

Vanguard ta rahoto cewa mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa’adu Abubakar III, ya yabawa gwamnatin Umar Namadi kan gudunmawar da ya ke bayarwa ga addinin Musulunci.

Alhaji Sa’adu Abubakar III ya yi kira ga al’ummar jihar da su ƙara himma wajen faɗakarwa kan fidda Zakka.

Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi ya yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar AZAWON da sauran hukumomi kan shirya taron wanda ya wayar da kan shugabanni da al'umma kan Zakka.

Jigawa ta yi fice wajen fidda zakka

A bara, an tara zakka ta kimanin Naira biliyan 1.3 daga yankunan masarautun Haɗejia, Dutse, da Kazaure, abin da ya sanya ake ganin jihar ta zama abin koyi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kirismeti: Gwamna Zulum ya yi wa ma'aikata gata a Borno

Gwamnatin Jigawa ta ce a dalilin haka ne ya sanya kungiyar ta shirya taron kasa har sau hudu a jihar.

An yi rabon zakka ga talakawa a Jigawa

Bayan taron, tawagar gwamna Namadi da Sarkin Musulmi sun ziyarci garin Lafiya, yankin ƙaramar hukumar Guri domin ƙaddamar da rabon zakka na wannan shekarar.

A rabon, an tara kayan amfanin gona da suka haɗa da shinkafa, gero, masara, dawa, da dabbobi masu darajar kimanin Naira miliyan 100 waɗanda aka rarraba ga mabuƙata.

Sarkin Musulmi ya yabawa garin Lafiya

Sarkin Musulmi ya yi kira ga sauran garuruwa da gundumomi da su yi koyi da al’ummar garin Lafiya wajen fidda Zakka da raba ta ga mabuƙata.

A ƙarshe, gwamna Namadi ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Jigawa za ta ci gaba da goyon bayan irin waɗannan shirye-shirye don ciyar da al’umma gaba.

An raba zakka a jihar Legas

Kara karanta wannan

Majalisar shura: Abba ya rabawa malaman musulunci kusan 50 mukamai a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa akalla mutane 306 ne suka ci moriyar shirin rabon zakkah da kungiyar Musulmi ta yankin Lekki ta yi.

Legit ta wallafa cewa an rabawa wadanda suka cancanta kayayyaki da kudi da yawansu ya haura N55m a jihar Legas yayin rabon kayan zakkar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng