Lokuta 3 da Gwamnatin Tarayya Ta Fifita Aminu Ado kan Sanusi II a Rikicin Sarautar Kano

Lokuta 3 da Gwamnatin Tarayya Ta Fifita Aminu Ado kan Sanusi II a Rikicin Sarautar Kano

A ranar 23 Mayu, 2024 ne gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta Kano ta tabbatar da tunbuke sarautar Sarki na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda Abdullahi Umar Ganduje ya nada.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya samu goyon bayan majalisar dokokin jihar wajen dawo da Sarkin Kano 14, Muhammadu Sanusi II, wanda tsohuwar gwamnati ta kora.

Tun bayan da gwamnatin Kano ta amince da dawo da darajar masarautar Kano kasar Sarki Ado Bayero, aka rika samun takun saka tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatin Kano.

Masarauta
Gwamnatin tarayya ta nuna wanda ta ke goyon baya a kujerar Sarkin Kano Hoto: Muhammad Sanusi II/Masarautar Kano
Asali: Facebook

Duk da a hukumance, babu inda gwamnatin Bola Tinubu ta fito karara wajen bayyana wanda ta ke goyon baya a matsayin Sarkin Kano ba, amma Legit ta tattaro lokuta uku da alamu su ka bayyana'

Kara karanta wannan

An daura auren fitaccen mawakin Kannywood: Ado Gwanja, Hamisu Breaker sun halarta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Dawo da Sarki Aminu jihar Kano

Legit ta ruwaito cewa Sarkin Kano 15 a ranar Alhamis, Aminu Ado Bayero ya dira a filin jirgin Malam Aminu Kano da misalin karfe 4.30 na safe inda dandazon masoya su ka tarbe shi.

Daga nan, tawagar jami'an tsaro, musamman sojoji ne su ka raka Sarkin fadar Nassarawa a ranar 25 Mayu, 2024 duk da korafin da gwamnatin jihar Kano ta yi a lokacin.

Mataimakin gwamna, Kwamred Aminu AbdulSalam ya zargi mashawarcin shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Rubadu da kitsa manakisar dawo da Aminu Ado Bayero jihar.

Nuhu Ribadu
Gwamnatin Kano ta zargi ofishin NSA da hannu a rikicin masarauta Hoto: Nuhu Ribadu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Nuhu Ribadu ya musanta zargin, har ya yi barazanar maka Aminu AbdulSalam a gaban kotu.

Ana zargin gwamnatin tarayya ce kadai ke da ikon bayar da irin yawan sojojin da su ka raka Aminu Ado Bayero karamar fada ta Nassarawa.

2. Ribadu ya kira Aminu halastaccen Sarkin Kano

Kara karanta wannan

Kotu ta dakile Ganduje, ta ba da umarni ga jami'an tsaro kan cafke kakakin Abba Kabir

Bayan musanta cewa ya na da hannu a sulalo da Sarki Kano na 15, Aminu Ado Bayero cikin jihar da asubahin ranar Asabar, Nuhu Ribadu ya sake nuna inda gwamnati ta karkata.

Daily Trust ta ruwaito cewa mashawarcin shugaban kasar ya kira Aminu Bayero da cewa shi ne halastaccen Sarki, duk da cewa batun ya na gaban kotu ana fafatawa.

Ya fadi haka ne bayan Sarki na 15 ya halarci wani taron ranar 3 Oktoba, 2024 a matsayin basarake daga jihar da ke fama da rikicin masarauta.

3. 'Yan sanda sun rufe kofar masarautar Kano

Hankula sun karkata a Kano bayan an wayi garin Juma'a, 6 Disamba, 2024 bayan an ga tarin jami'an tsaron DSS da motocin yaki sun tare kofar Kudu ta Fadar Muhammadu Sansui II.

An samu rahoton cewa Sarkin ya yi niyyar fita domin raka sabon hakimin Bichi kasarsa, amma jami'an tsaron sun hana shiga ko fita daga fadar.

Kara karanta wannan

'Saurin me ake yi?" Dattawan Arewa sun shawarci gwamnati kan kudirin harajin Tinubu

Gwamnatin Kano ta yi tir da lamarin, domin ya daga hankulan wasu daga cikin mazauna kusa da masarautar, inda su ka shiga zaman dar-dar.

Gwamnatin tarayya ta yi gum da bakinta a kan lamarin, domin hatta rundunar 'yan sandan Kano ba su bayyana dalili ko wanda ya bayar da umarnin rufe kofar masarautar ba.

An yi hukunci a kan rikicin masarautar Kano

A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun jiha da ke zamanta a Kano ta yanke hukunci a kan dambarwar masarautar tun bayan Sarki Aminu Ado Bayero ya ki amincewa da sauke shi.

Kotun karkashin Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta haramta wa Aminu Ado Bayero da bayyana kansa a matsayin sarki, sannan ta tabbatar da nadin Muhammad Sanusi a matsayin Sarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.