'Sauran Matsorata ne': Dogara Ya Fadi Irin Shugaban da Najeriya Take So, Ya Yabawa Tinubu
- Tsohon shugaban Majalisar Tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya sake magana kan halin da ake ciki a Najeriya
- Dogara ya yabawa salon mulkin Bola Tinubu musamman wurin dogewa kan tsare-tsaren da ya kawo
- Tsohon dan Majalisar ya ce tsoron shugabannin baya a Najeriya ya jefa ta a mummunan hali da ake fuskanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya yi magana kan salon mulkin Bola Tinubu.
Hon. Dogara ya ce yana goyon bayan gyare-gyaren da Tinubu ya kaddamar saboda a ganinsa su suka fi dacewa da Najeriya.
Dogara ya yabawa salon mulkin Tinubu
Dogara ya yi wannan jawabi a wajen bikin yaye dalibai karo na 14 na Jami’ar Achievers da ke Owo a jihar Ondo, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon dan Majalisar ya bayyana cewa Tinubu ya nuna jarunta a matsayin jagora “mai shirin jagoranci cikin jaruntaka".
Ya ce shugaban ya dauki matakan ko da kuwa hakan zai zo da matsalar kudi ko kalubale a kansa, Punch ta ruwaito.
Dogara ya ce jinkiri wajen aiwatar da gyare-gyaren haraji da sauran shirye-shirye na cigaba zai zama alamar tsoro.
Tsare-tsare: Dogara ya kira Tinubu da jarumi
Yakubu Dogara ya kara da cewa rashin samun jagoran da ke da jaruntaka ya jefa kasar cikin yanayi na rashin cigaba a bangaren tattalin arziki.
Tsohon kakakin Majalisar ya ce kasar na gudanar da irin jagoranci na mayar da martani, maimakon jagoranci na kirkire-kirkire da hangen nesa.
“Yin biyayya ga ra’ayi marasa tushe saboda wahalhalu sun yi yawa, kuma a ce a janye, alama ce ta tsoro, yanzu muna da jagora mai jaruntaka."
- Yakubu Dogara
Dogara ya magantu kan cire tallafin man fetur
A baya, kun ji cewa tsohon shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya bayyana cewa babu laifin shugaba Bola Tinubu a cire tallafin mai.
Rt. Hon. Dogara ya ce tun kafin hawan Tinubu mulki aka cire tallafin mai a Najeriya kawai shi ya tabbatar da haka ne a baki.
Asali: Legit.ng