Tinubu Sun Tafi Bikin Gidan Barau, Shettima da Dangote Sun Halarci Auren Bagudu
- Manyan mutane sun ziyarci Kaduna da Ministan kasafin kudi ya aurar da yaronsa ga ‘yar gidan Tatari Ali
- Ibrahim A. Bagudu ya angonce da Amina Tatari Ali bayan an shafa fatiha a masallacin Sultan Bello a jiya
- Tun daga mataimakin shugaban kasa, gwamnoni har zuwa Aliko Dangote, auren bai bar manyan mutane ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - A lokacin da Disamba ta zo, an saba ganin daurin aure iri-iri a Najeriya. A shekarar nan ma dai abin bai canza ba.
An saba yin aure a karshen shekara a kasar nan saboda lokacin hutu, daukewar ruwa, sannan kuma mutane sun fara cin kaka.
Ibrahim Bagudu ya auri Amina Tatari a Kaduna
Rahoton da Daily Trust ta fitar ya nuna Ibrahim A. Bagudu ya auri Amina Tatari Ali a Kaduna, kuma mutane sun halarci bikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Juma’a, 13 ga watan Disamba 2024, aka daure aure tsakanin ‘dan ministan kasafin kudi da ‘yar gidan Tatari Ali.
Auren 'ya 'yan Atiku Abubakar Bagudu a baya
A 2018 lokacin yana gwamnan Kebbi, Bagudu ya aurar da ‘dan sa Abdullahi Musa ga Habiba Umar a karamar hukumar Jega.
Bayan nan kuma a Agustan 2022, tsohon gwamnan na Kabbi ya aurar da wata diyarsa, wannan karo ma dai abin ya yi armashi.
Su wanene suka halarci auren a Kaduna?
Mai girma mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima yana cikin wadanda suka tofawa daurin auren na yau albarka.
Sauran wadanda suka halarci auren sun hada da gwamnonin Borno, Kaduna da Kebbi; Babagana Zulum, Uba Sani da Nasir Idris.
Haka zalika mai kudin nahiyar Afrika, Aliko Dangote, yana Kaduna wajen daurin auren. An ga Ahmad Aliyu da Abbas Balarabe Lawal.
Sauran manyan baki sun hada da gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da kuma takwarsa na jihar Nasarawa watau Abdullahi Sule.
Har ila yau an ga abokan aikin mahaifin ango kamar Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da kuma na kudi, Wale Edun.
Limamin masallacin Sultan Bello, Dr. Muhammad Suleiman Adam, ya daura auren Ibrahim Atiku Bagudu da sahibarsa, Amina Tata.
A shafinsa na X, Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya wallafa hotunansu wajen auren.
Haduwar yaron tsohon gwamnan Kaduna da Oshiomhole
A makon da ya gabata aka ji labari Hon. Bello El-Rufai ya ba da labarin haduwar shi da Adams Oshiomhole a zauren majalisar tarayya.
‘Dan siyasar wanda ya taba zama shugaban APC na kasa ya tambayi Bello El-Rufai game da mahaifinsu watau Malam Nasir El-Rufai.
Asali: Legit.ng